Tarin Lala
Tarin Lala, wanda ake kira pertussis ko kuma tarin na kwana 100, cuta ce mai yawa, da za a iya kawar da ƙwayoyin cuta. Alamar farko sau da yawa tana kama da na sanyi kamar yoyon hanci,zazzzabi da kuma yin tari kadan-kadan, amma bayan haka, za a yi watanni biyu ko uku na matsanancin tarin, Mutum zai yi ta amai, ya karya awazu, ko kuma ya gaji sosai daga ƙoƙarin yin tarin. Yara da ba su kai shekara ɗaya ba tarin lala na iya jaznyo masu rashin iya yin numfashi,Lokacin tsakanin kamuwa da cutar tarin lala da somawar alamun sau da yawa kwanaki bakwai zuwa goma ne,Ciwon zai iya faruwa a waɗanda aka yi musu rigakafi, amma alamun ba su da sauƙi.
Ana maganin tarin lala ta hanyar Shan kwayoyin magunguna da ake kira Macrolides, misalinsu sune erythromycin, azithromycin da dai sauransu