Tapiwa Gambura marubuciya ce sannan Kuma tana daukar foto (wato photographer). Kuma An haife tane a Johannesburg, Afirka ta Kudu. Al'adu na daya daga cikin abin da aikin ta yake haskawa wajen yin hasashen halin da Africa zata tsnci kanta a cikin a karni na ashiri da daya. Bayan rubutu, Tapiwa ta kasance jaruma a masana'antar fina-finai kuma mawakiya ce. Sannan ta bada muhimmiyar gudun mawa a fannin adabi a Africa. Wasu ayyukan da tayi ya taimaka wajen yaduwar sunan ta har ta samu dama aka gayyaceta tattaunawa a Independent Zimbabwe organization a shekara ta 2015 da kuma 2017.

Ta karbi kyaututtuka da dama daga National institute Of Allied Act da suka shafi rubutu da kuma wasan kwaykwayo. Tapiwa ta yi imani da cewa zata yi amfani da baiwar ta wajen bada gudunmawa ga mutanen nahiyar Afrika.

Manazarta

gyara sashe