Tambayoyi Guda Hudu Da Za Ai wa Kowa Ranan Alqiyama

TAMBAYOYI GUDA HUDU DA ZA A YIWA KOWA A RANAR ALKIYAMA

Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Ranar alkiyama digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an yi masa tambayoyi guda hudu:

◾ Rayuwarsa: A me ya karar da ita

◾ Iliminsa: Me ya aikata  da shi

◾ Dukiyarsa: A ina ya same ta, kuma yaya ya kashe ta

◾ Gangar jikinsa: Yaya ya yi amfani da ita."

   Tirmidhi:2417, Darimi:537

Kowa sai ya yi shirin amsa wadannan tambayoyi.