Tambayan Wata Baya Badiya Akan Azabar Kabari

🌺🌺🌺

Wata bayahudiya ta shiga wajen Nana Aisha رضى الله عنها sai ta yi magana a kan azabar kabari, sai ta ce, Allah ya kare ki daga azabar kabari. Sai Nana Aisha ta tambayi Annabi صلى الله عليه وسلم game da azabar kabari. Annabi صلى الله عليه وسلم sai ya ce mata, "azaba a kabari gaskiya ne". Nana Aisha رضى الله عنها ta ce, tun daga wannan lokaci, duk lokacin da Annabi صلى الله عليه وسلم ya yi wata Salla sai ya nemi tsari daga azabar kabari". Bukhari:1372, Muslim

Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:"Idan maza suka dauki janaza (gawar mutum) a kafadunsu, idan mutumin/mutuniyar kirki ne/ce sai ya dinga cewa, ku gabatar da ni, ku gabatar da ni (a yi sauri a kai shi). Idan kuma ba mutumin/mutuniyar kirki ba ce sai ta dinga cewa, na halaka! Ina zaku kai ni? Kowane abu yana jin abin da gawar take cewa amma ban da mutum. Da dan Adam zai ji abin da yake/take fada da ya suma". Bukhari:1380, Nasà'i

                 🌺🌺🌺