Taher Mohamed Ahmed Taher Mohamed Mahmoud (an haife shi ranar 7 ga watan Maris, 1997) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Masar, wanda ke taka leda a ƙungiyar Al Ahly ta Masar da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Masar a matsayin ɗan wasan gefe.[1][2]

Taher Mohamed
Taher Mohamed acikin taro tare da ambassador din kasashin waje

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Ya buga wasansa na farko a ƙungiyar kwallon kafa ta Masar a ranar 16 ga Nuwamba 2018 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika da Tunisia, a matsayin wanda ya maye gurbin Amr Warda na mintuna na 86.[3] Taher yana cikin jerin 'yan wasan karshe na 'yan wasan Olympics na Masar da suka lashe kofin Afirka na baya-bayan nan da aka gudanar a birnin Alkahira a watan Nuwamban shekarar 2019 kuma ya yi nasarar tsallakewa zuwa Tokyo 2020.