TABBATAR DA SHIGAR WATAN RAMADAN

TABBATAR DA SHIGAR WATAN RAMADAN

Shugowar watan Ramadan yana tabbata ne da dayan lamri biyu: Na farko: Cikkar watan da ya gabace shi (kwana talati) wato Sha’aban. Idan sha’aban ya cika kwana talatin, rana ta talatin da daya yini ne na Ramadan kai tsaye.

Na Biyu: Ganin jinjirin watan Ramadan, idan aka ga jinjirin watan Ramadan a daren talatin na wannan wata. Domin fadin Allah madaukakin sark

﴿ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهرَ فَليَصُمهُ ١٨٥﴾

Ma’ana: “Duk wanda ya shaidi (shigar) watan Ramadan to ya azumce shi”. (Bakara 185).

 Haka kuma da fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Idan ku ka ga jinjirin wata to ku yi azumi, kuma idan ku ka ganshi ku aji ye, idan kuma an boye muku ta (dalilin giragizai) ku cika shi talatin”. (Bukhari, Muslmi).

 Idan mutanen wani gari suka ga watan azumi ya wajaba gare su. Kamar yadda yake fitar wata yana sabawa, fitar wata a yakin Asiya daban yake da yadda fitar shi take a yankin Turai da Afrika bah aka yake ba a latin Amirka misali. Da haka ne ko wanne yanki da bangare na duniya suke da hukuncin da ya kebance su. Idan kuma al’ummar musulmai suka yi azumi da ganin wata daya to wannan shi ne abin da ya fi kyautatuwa da bayyana hadin kai da kuma ‘yan uwantaka.

 Ganin watan mutun daya adali ya wadatar ko biyu, kamar lokacin da Manzon Allah ya halasta ganin watan mutum daya na Ramadan (Muslim ne ya ruwaito). Amma na ajiye azumi (wato watan sallah) sai da ganin adalai biyu, kamar yadda Manzon Allah ﷺ‬ bai halatta ganin adili daya ba a lokacin ajiye https://islamhouse.com/read/ha/fikhu-a-sawwake-2778721