Sunnar Annabi Muhammad (S,AW) Lokacin tashi daga

🍂🍂🍂

SUNNAR ANNABI SAW LOKACIN TASHI DAGA BACCI

🍂 Annabi صلى الله عليه وسلم ya kasance idan ya tashi daga bacci yana cewa:

"الحمد لله الذي أحيانا بعد ما اماتنا وإليه النشور"

                     Bukhari

🍂 Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya tashi daga bacci kada ya sanya hannunsa cikin  mazubin (ruwa)" har sai ya wanke hannunsa sau uku. Saboda bai san a ina hannunsa ya kwana ba". Bukhari Muslim

A yanzu yawanci ba a budadden abu ake yin alwala ba, duk da haka sunna ne idan mutum ya tashi daga bacci ya fara wanke hannunsa sau uku.

🍂 Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya tashi daga bacci ya shaka ruwa a hancinsa ya face sau uku, domin shaidan yana kwana a hancinsa". Muslim

Sunna ne shi ma idan ka tashi daga bacci, bayan ka wanke hannu ka debi ruwa ka shaka ka face sau uku.

Sheikh Uthymeen yana cewa: "Allah سبحانه وتعالى zai iya sanya shaidan ya kwana a hancin mutum saboda wata hikima. Shi yasa Annabi صلى الله عليه وسلم ya yi umarni da a shaka ruwa a face sau uku. Wannan kuma ba shaka ruwa ba ne na alwala"

Wasu malaman suna cewa ko da ba alwala mutum zai yi ba (kamar mace lokacin al'adarta), zai shaka ruwa ya face.

والله تعالى اعلم

                          🍂🍂🍂