Sihem Amer-Yahia
Sihem Amer-Yahia kwararriya ce 'yar ƙasar Aljeriya ce masaniyar kwamfuta. Ita ce Daraktan Bincike na CNRS a Laboratoire d'Informatique de Grenoble. Tana jagorantar ƙungiyar bincike ta SLIDE.[1] Sihem Amer-Yahia tana aiki akan sarrafa bayanai,[2] yaruka n bayyanawa da algorithms na sarrafa tambaya. Abubuwan da ta wallafa sun haɗa da crowdsourcing, computational complexity, data analysis, data handling, data visualisation, information science, da magance sabbin matsalolin sarrafa bayanai a cikin intanet masu zuwa da manyan aikace-aikacen bayanai.[3]
Sihem Amer-Yahia | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Aljir, 1972 (51/52 shekaru) | ||
ƙasa | Aljeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Paris-Sud (en) Ecole Nationale Supérieure d'Informatique (en) Paris Dauphine University (en) Institut National de Recherche en Informatique et en Automatique (en) | ||
Thesis director | Claude Delobel (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | computer scientist (en) da researcher (en) | ||
Kyaututtuka |
gani
|
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAmer-Yahia ta sami Ph.D. a CS daga Paris-Orsay da INRIA a cikin shekarar 1999, [4] da Diplôme d'Ingénieur daga INI, Algeria.
Sana'a
gyara sasheKafin ta shiga CNRS, Amer-Yahia ta yi aiki a matsayin Babbar Masaniyar Kimiyya a QCRI, Babbar Masaniyar Kimiyya a Yahoo! Research da Memba na Ma'aikatan Fasaha a AT&T Labs.[5]
Amer-Yahia tayi aiki a kwamitocin jaridu da dama ciki har da kwamitin zartarwa na SIGMOD. Tana ɗaya daga cikin amintattun Kyautar VLDB.[6]
Amer-Yahia kuma ta yi aiki a Hukumar EDBT (Extending Database Technology), kuma ita ce shugabar kwamitin shirye-shirye na taron EDBT a shekarar 2014. Ita ce Babbar Editan Jaridar VLDB na Turai da Afirka.[7]
Ta kasance editan haɗin gwiwa na ACM TODS, lokacinta yana ƙarewa a cikin shekarar 2017, kuma ta kasance editan yanki na Jaridar Systems Systems. [8]
Kyaututtuka da karramawa
gyara sasheA cikin shekarar 2020, Amer-Yahia ta sami Medal Azurfa na CNRS.[9]
A cikin 2017, an gane Amer-Yahia a matsayin fitacciyar memba na ACM.[10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Sihem Amer-Yahia | Laboratoire d'Informatique de Grenoble" . Retrieved 2020-03-08.
- ↑ "BICOD 2017" . www.dcs.bbk.ac.uk . Retrieved 2020-03-08.
- ↑ "Sihem Amer-Yahia as an IEEE author" . Retrieved 2020-03-08.
- ↑ Amer-Yahia, Sihem (1999-01-01). Du chargement en masse dans une base de donnees (en general) et de la migration relationnel-objet (en particulier) (thesis thesis). Paris 11.
- ↑ "Sihem Amer-Yahia - Home" . dl.acm.org . Retrieved 2020-03-08.
- ↑ "Board of Trustees" . www.vldb.org . Retrieved 2020-03-08.
- ↑ "The VLDB Journal" . Springer. Retrieved 2020-03-08.
- ↑ Information Systems Editorial Board .
- ↑ "Médailles d'argent 2020 | CNRS" (in French). CNRS. 13 February 2020. Retrieved 2020-03-08.
- ↑ "Sihem Amer-Yahia" . awards.acm.org . Retrieved 2020-03-08.