Siffar Sallah Annabi Muhammad SAW

🌹🌹🌹

SIFFAR SALLAR ANNABI (SAW) (1)

"صلو كما رأيتموني أصلي"

"Ku yi Sallah kamar yadda ku ka ga ina yi"

🌹Yin kabbara da dora hannaye bisa kirji

Bayan Annabi صلى الله عليه وسلم ya yi alwala ya kyautata ta, sai ya fuskanci alkibla. A nan babu wata niyyar Sallah da za ka fada, misali, ka ce, na yi niyyar yin sallar azahar raka'a hudu. Annabi صلى الله عليه وسلم bai yi haka ba, bai kuma bayar da umarni a yi ba. Tun daga lokacin da ka tsaya, ka yi kabbara ka san me kake shirin yi, wannan ita ce niyya, ba sai ka furta ba.

Bayan Annabi صلى الله عليه وسلم ya fuskanci alkibla, sai ya fara yin sallah. Akwai hanyoyi guda uku da Annabi صلى الله عليه وسلم yake fara bude sallar sa da su:

🔸 Annabi صلى الله عليه وسلم yana daga hannayensa tare da yin kabbarar harama "Allahu Akbar", yana daga hannayen zuwa daidai kafadunsa. Bukhari:738


🔸 Wani lokacin kuma bayan ya yi kabbara ya ce: "Allahu Akbar" sai kuma ya daga hannayensa. Bukhari, Nasà'i

🔸 Wani lokacin kuma sai ya daga hannayensa, sannan sai ya ce: "Allahu Akbar". Bukhari, Abu Dàwud

Annabi صلى الله عليه وسلم yana daga hannayensa 'yan yatsun suna mike, ba ya wara su, kuma ba ya hade su (tsaka-tsaki). Wani lokaci kuma yana daga hannayensa su wuce fatun kunnuwansa. Sai kuma ya dora hannunsa na dama a kan na hagu. Bukhari, Muslim, Abu Dàwud, Ibn Khuzaimah

A wata ruwayar Annabi صلى الله عليه وسلم ya kasance yana dora (tafin) damansa a kan bayan hannunsa na hagu, ko ya dora shi a wuyan hannu ko bisa dantse, sai kuma ya dora su a kan kirjinsa. Yana kuma umartar sahabbansa da yin haka. Sifati salatin Nabiy:77

🌹 Tsayuwa domin karatu

Bayan Annabi صلى الله عليه وسلم ya yi kabbara sai ya sunkuyar da kansa ya dubi kasa daidai inda zai yi sujjada. Yin hakan zai sa mutum ya samu nutsuwa da khushu'i a cikin sallah. Sai kuma ya karanta azkar na fara sallah da ake cewa "du'aul istiftahi". Akwai azkar da dama da Annabi  صلى الله عليه وسلم yake bude sallarsa da su, wani lokaci ya fadi wannan, wani lokacin ya fadi wancan, yana karanta su tsakanin yin kabbarar harama da fara karatu.

Daga cikin su Annabi صلى الله عليه وسلم yana cewa:

"Allahumma bà'id bainiy wa baina khadàyàya kamà bà'adta bainal mashriqi wal magribi. Allahumma naqqini min khadàyàya kamà yunaqqath-thaubul abyadhi minad danas. Allahummag-silnii min khadàyàya bil mà'i wath-thalji wal barad. Bukhari, Muslim

Bayan ya karanta addu'ar bude sallah, sai kuma ya nemi tsarin Allah سبحانه وتعالى daga shaidan sai ya ce: "A'uzu billahi minash-shaidanir rajiim, min hamzihi wa nafkhihi wa nafathihi".

Wani lokaci kuma ya ce: A'uzu billahis-samii'il aliim minash-shaidanir rajiim" .....

Sai kuma ya karanta Bismillahir Rahmanir Raheem".

A duk sallolin da ake yi a bayyane ko a asirce dukkansu Annabi صلى الله عليه وسلم ba ya yin addu'ar bude sallah da neman tsari daga shaidan da yin "Bismillah" a sarari, duka a asirce yake yin su.

Bayan nan, sai Annabi صلى الله عليه وسلم ya karanta fatiha, ya kasance yana girmama sha'aninta, yana cewa: "Babu sallah ga wanda bai karanta fatihatil kitab a cikinta ba". Bukhari:756, Muslim

A wani hadisin kuma Annabi صلى الله عليه وسلم yana cewa: "Sallar mutum ba ta cika ba idan bai karanta fatiha a cikinta ba". Muslim

Saboda haka wajibi ne karanta fatiha a kowace raka'a.

Idan mutum yana bin liman sallah, Annabi صلى الله عليه وسلم ya hana yin karatu ga wanda yake bin liman, a cikin sallar da ake bayyana karatu. Amma a sallar kuma da ake boye karatu, mamu zai iya yin karatu. Sifati Salatin Nabiy:86

Idan Annabi صلى الله عليه وسلم ya gama karatun fatiha, sai ya daga muryarsa ya ce: "Àmeen".

Bayan Annabi صلى الله عليه وسلم ya gama karatun fatiha, sai ya karanta wata sura daga cikin Alqur'ani mai girma. Wani lokaci yana tsawaita karatu, wani lokacin kuma yana gajarta shi saboda wani dalili, kamar a halin tafiya, ko tari ya kama shi, ko idan ya ji kukan yaro.

Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Zan fara sallah ina da nufin in tsawaita ta, amma idan na ji kukan yaro sai na gajarta ta, saboda na san yadda mahaifiyarsa take damuwa da kukansa".

A wani lokaci Annabi صلى الله عليه وسلم yana karanta Suratul Mu'uminun a sallar asuba lokacin da ya zo ayar da take magana akan Annabi Musa da Annabi Hàrun عليهما السلام sai tari ya kama shi sai ya yi ruku'u". Bukhari

               الله تعالى اعلم

✍🏻 Umm Khaleel

                           🌹🌹🌹