Shkodran Mustafi
Shkodran Mustafi (An haifeshi a ranar 17 ga watan Aprilu shekara ta alif 1992), tsohon dan wasan baya ne na kasar Jamus.
Shkrodan Mustafi | |
---|---|
sunan gida | |
Bayanai | |
Suna a harshen gida | Mustafi |
Tsarin rubutu | Baƙaƙen boko |
Cologne phonetics (en) | 6823 |
Mustafi ya fara buga kwallon kafa tun yana dan karami. Ya fara buga wasanni a samartakar sa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Harmburger SV da kungiyar kwallon kafa ta Everton inda ya buga wasa daya a wasan da ya shigo daga baya kafin ya koma ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sampdoria a shekarar alif 2012. Ya sanya hannu har na tsawon shekaru 5 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Valencia a watan Ogusta 2014.[1] Sai kuma ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal akan jumillar kudi £35 miliyan bayan shekaru 2. inda ya bu
ga wasanni guda 151 a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Daga baya kuma ya koma gasar Bundesliga inda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Schalke04, sai kuma gasar Laliga inda ya doka wasa a kungiyar kwallon kafa ta Levente.[2]
A fannin kasa kuma Mustafi ya fara buga cikakken wasan shi inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta kasar Poland yayin da ya wakilci kasar tashi wato kasar Jamus a shekara ta alif 2014. Kuma yana daya daga cikin jerin yan wasan da suka buga gasar cin kofin duniya na shekarar alif 2014 da aka buga kuma sune suka samu nasara a gasar. Da gasar kofin FIFA Confederation wanda aka buga a shekarar alif 2017. Da kuma gasar UEFA Euro wanda aka buga a shekarar alif 2016.[3]
Rayuwar Gida
gyara sasheMustafi dan asalin kasar Albaniya ne daga Gostivar kudancin Marcedonia ya tasa kuma yayi wayo a kasar Jamus. Saidai dan wasan ya rike shaidar zama dan kasa na kasashen biyu da Albaniya da kuma ƙasar Jamus.[4]
Mustafi ya kasance yana yin addinin musulunci.
A watan Yuli shekarar alif 2016 ya auri mata yar Tsatsan kasar Albaniya mai suna Vjosa Kaba a Gostivar.[5] Ma'auratan sun hafi diya mace inda suka sanya mata suna Noemi (an haifeta a watan Yuli 2007) sai kuma suka haifi namiji sau suka sa suna Amar wanda aka haifeshi a watan Junairu shekarar alif 2019.[6][7]
Girmamawa
gyara sasheArsenal
FA Cup: 2016–17, 2019–20[67][68]
EFL Cup runner-up: 2017–18[69]
UEFA Europa League runner-up: 2018–19[70]
Germany U17
UEFA European Under-17 Championship: 2009[71]
Germany
FIFA World Cup: 2014[72]
FIFA Confederations Cup: 2017[73]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Shkodran Mustafi: Profile". worldfootball.net. HEIM:SPIEL. Retrieved 29 June 2020.
- ↑ Panorama-sport (22 January 2014). "Shkodran Mustafi, "blerja" e kombetares". Panorama sport. Archived from the original on 25 January 2014. Retrieved 22 January 2014.
- ↑ Valencia beats Villarreal 3–1 to move 2nd in Spain". Associated Press. 2 November 2014. Retrieved 2 November 2014.
- ↑ Davis, Callum (5 October 2016). "Shkodran Mustafi reveals the importance of his Muslim faith". The Daily Telegraph. Archived from the original on 12 January 2022. Retrieved 7 October 2016.
- ↑ "Mustafi gibt Ja-Wort" [Mustafi says yes]. Hessenschau. 29 July 2016. Archived from the original on 13 August 2016. Retrieved 20 July 2017
- ↑ "Shkodran Mustafi wife - Vjosa Kaba". ohmyfootball.com. Retrieved 10 February 2021
- ↑ "Hurra! WM-Held Mustafi ist Papa geworden". T-Online (in German). Retrieved 20 July 2017.