Sherif Boubaghla ko Cherif Boubaghla (da larabci : الشريف بوبغلة, mutumin da yake da alfadari ) (cikakken suna Muhammad Al-Amjad bin Abd Almalik محمد الأمجد بن عبد المالك) ya kasance shugaban juriya na sojojin Algeria Wanda ya jagoranci gwagwarmaya da mamayar Turawan mulkin mallaka na Faransa a tsakiyar karni na 19. [1]

Sherif Boubaghla
Rayuwa
Haihuwa 1820
Mutuwa 26 Disamba 1854
Sana'a
Hoton sharif

Mutuwar sa

gyara sashe

A ranar 21 ga watan Disamba, shekarar 1854, wani dan leken asirin Algeria da ke aiki da Faransa ya raunata Cherif Boubaghla. Ya faɗi a kan ƙasa mai laka, sannan ɗan leƙen asirin ya kashe shi ya Kuma yanke kansa ya kai shi ga mai mulkin Faransa na Lardin Bordj Bou Arréridj. Mai mulkin faransa ya kafa kan Cherif Boubaghla a kan sanda don mutanen Algeria su gan shi. [2] [3] Bayan wannan Faransawan sun ɗauki kai zuwa Faransa.

Komawar kokon kansa daga Faransa

gyara sashe

A ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2020 Aljeriya ta karɓi ragowar kwankunan kawunan 24 masu gwagwarmaya da mulkin mallaka na Algeria. Daga cikin wadannan akwai kokon kan Sheikh Bouzian da kwanyar shugaban adawa Mohammed Lamjad ben Abdelmalek, wanda aka fi sani da Cherif Boubaghla . [4] [5]

Duba kuma

gyara sashe
  • Mamayewar Algiers a 1830
  • Abdelkader al-Jazairi
  • Cheikh Bouamama
  • Tawayen Mokrani
  • Yakin Aljeriya

Manazarta

gyara sashe
  1. Cinema and the Algerian War of Independence: Culture, Politics, and Society
  2. Cherif Boubaghla and Sheikh Bouziane symbols of popular resistance against the French occupation
  3. "Secret-of-move-the-martyr-Sharif-Boubaghla to France(ar)". Archived from the original on 2020-07-20. Retrieved 2021-03-04.
  4. France returns remains of Algerian anti-colonial fighters
  5. "France returns skulls of Algerians who fought colonisation". Archived from the original on 2020-11-13. Retrieved 2021-03-04.

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe