Shamsuabbaty
TAMBAYA TA 1: Wane irin albishir Manzon Allah (SAW) yake yi wa al`ummarsa kafin watan Ramadan ya kama?
AMSA: Manzon Allah (SAW) ya Kasance yana yi wa al`ummarsa bushara da zuwan Ramadan. Kamar yadda hadisi ya tabbbata daga Abu Huraira ya ce: na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: إِذَا دَخَلَ رَمَضَانُ فُتِّحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ وَغُلِّقَتْ أَبْوَابُ جَهَنَّمَ وَسُلْسِلَتْ الشَّيَاطِينُ Ma’ana: Idan watan Ramadan ya shigo ana bude kofofin rahama da kofofin aljanna, kuma ana rufe kofofin jahannama, kuma ana daure shaidanu. Haka kuma an ruwaito daga Anas Ibn Mālik ya ce: (Watan) Ramadan ya shigo sai Manzon Allah r ya ce: إن هذا الشهر قد حضركم وفيه ليلة خير من ألف شهر من حرمها فقد حرم الخير كله ولا يحرم خيرها إلا محروم Ma’ana: Hakika wannan wata (na Ramadan) ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin da ke cikinsa) hakika an haramta masa alkhairi dukansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa sai wanda bashi da rabo.