Selanchi ( Amharic: ስለ አንቺ) fim ne na wasan kwaikwayo da soyayya na Habasha da aka shirya shi a shekarar 2009. Belay Getaneh ne ya bada umarni, ya fito tare da Sayat Demissie da Leoul Solomon. Labarin ya ta'allaka ne a kusa da Wondwossen mai shekaru 20, wanda ke fama da taɓin hankali kuma ya kamu da sha'awar Fikir. Dukansu biyun sun hana su aiwatar da dangantakarsu saboda kin mahaifin Wondwossen, Laftanar Janar wanda ke kula da shi. Fim ɗin ya lashe kyautattuka uku a bikin fina-finai na ƙasar Habasha karo na huɗu kuma shi ne ya lashe kyautar mafi kyawun wasan barkwanci na ƙasa da ƙasa a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na New York.[1]

Selanchi
Asali
Asalin harshe Amharic (en) Fassara
Ƙasar asali Habasha
Characteristics
Genre (en) Fassara romantic comedy (en) Fassara
'yan wasa

Labarin fim

gyara sashe

Wondwossen, ɗalibin makarantar sakandare mai shekara 20, yana fama da matsalar taɓin hankali, sakamakon tsananin kulawa da mahaifinsa ya yi masa wanda ya hana shi shiga cikin zamantakewar. Mahaifinsa Laftanar Janar ne wanda ke aiki a Amurka Blackjack Online. A lokacin da yake makaranta, ya sami wata yarinya daga unguwarsu mai suna Fikir. Ba kasafai suke da lokacin yin soyayya ba tare da gujewa sanin mahaifinsa ba. A karshen labarin, mahaifinsa ya san abin da suka yi, amma ya cika da mamaki lokacin da Fikir ya ba da labari mai ban tsoro kuma ya bayyana gaskiyarta ga Wondwossen. A ƙarshe sun kasance da haɗin kai a matsayin iyali.[1]

Kyautattuka

gyara sashe

Fim ɗin ya lashe kyautattuka uku a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na Habasha karo na huɗu kuma ya sanyawa suna Best International Romantic Comedy Feature a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na New York.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Silanchi". www.ethiopianfilminitiative.org. Retrieved 2021-06-13.
  2. Tafesse, Serkalem (17 August 2018). "Films of Powerful Love Stories in Ethiopia". Culture Trip. Retrieved 2021-06-14.