Sarautar Ebiraland

Sarkin gargajiya na mutanen Ebira

Ohinoyi na Ebiraland shine sarkin gargajiya na mutanen Ebira. Sunan Atta na Ebiraland shima a tarihi an yi amfani da shi don wannan matsayi amma ya kasa samun tagomashi a ƙarni na 20.[1] Gungun dattawa ne suka zaɓi wannan matsayi kuma a al'adance (wanna matsayi) yakan koma tsakanin manyan dangin Ebira.[2] Ohinoyi na yanzu, shi ne mai girma, Alhaji Dr. AbdulRahman Ado Ibrahim ya fara mulki ranar 2 ga watan Yuni, a shekara ta 1997.[3]

Infotaula d'esdevenimentSarautar Ebiraland
Iri title (en) Fassara

Jerin Sarakunan Ebiraland

gyara sashe
  • Omadivi Abonika (wanda ba a sani ba-1917), ya yi sarauta 1904-1917
  • Ibrahim Onoruoiza (1884-1964), yayi mulki 1917-1954 (ya yi murabus)
  • Muhamman Sani Omolori, (1919-1990), yayi mulki 1957-1997
  • Abdul Rahman Ado Ibrahim (haihuwa 1929-2023) 1997-2023.

Manazarta

gyara sashe
  1. Sarki, Idris Enesi (1996). The Ohinoyi throne: towards peaceful successions. Samaru, Zaria: S. Asekome. p. 15.
  2. Osaghae, Eghosa E.; Ibeanu, Okechukwu; Onu, Godwin; Gaskia, Jaye; Jibo, Mvendaga; Galadima, H. S.; Isumonah, Victor; Simbine, A. T. (2001). Ethnic groups and conflicts in Nigeria. 4. Ibadan: University of Ibadan. p. 113.
  3. Ajanah, Nuhuman (1997). Ebiras at a Glance. 2. Nigeria: Numa. p. 37.

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin jihohin gargajiya na Najeriya