Sakamako Mai dasa Bishiyoyi Akan Hanya

SAKAMAKON WANDA YAKE DASA ITACEN KAYAN MARMARI KO BISHIYU

Daga Anas (Allah Ya ƙara masa yarda) ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce:

"Babu wani musulmi da zai dasa wani abun dashe ko ya shuka wani abun shukawa; sai tsuntsu ko mutum ko wata dabba su ci daga wannan abun da aka shuka ɗin, face ya zame masa ladan sadaƙa."

_Imamul Bukhari da Muslim_