Hajiya Sa'adu Muhammad Ka'oje Ta kasance mai san ganin yara Maza da Mata sun samu ingantaccen ilimi da cigaba a rayuwarsu.[1]

Haihuwa gyara sashe

Sa’adatu Muhammad Ka’oje an haife ta a shekarar 1972 a Unguwar Titin Koko a Sakkwaton Najeriya.

Karatu gyara sashe

Tayi karatun firamere a Makarantar Model da ke kan titin Birnin Kebbi wacce a yanzu aka fi sani da Makarantar Kimiyya ta Yakubu Mu’azu. Bayan ta gama aka kaita Kwalejin Tarayya da ke Okigwe a Jihar Imo ta fara makarantar sakandare a can kafin a mayar da ita Kwalejin Tarayya ta Gusau inda ta kammala karatun sakandire. Bayan nan ta shiga Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari inda ta samu takardar shaidar ilimi ta kasa (NCE). Daga nan ta wuce Jami’ar Usman Dan Fodiyo duk a Sakkwato ta samu shaidar digiri na farko, bayan ta kammala ne ta fara aiki da makarantu masu zaman kansu daga nan ta samu aikin malanta a makarantun gwamnati.[2]

Shugabanci gyara sashe

Ita ce Shugabar makarantar Firamare da ke Ƙaramar Sakandare ta Turaki da ke kan Titin Sarki Yahaya a birnin Sakkwato.

Manazarta gyara sashe

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-04. Retrieved 2022-10-04.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-04. Retrieved 2022-10-04.