Robin baba, Farfesa Ɗangambo ya siffanta shi da, yabon da maroƙi ke yiwa gwaninsa ta hanyar yabonsa da kyawawan halaye, asali, kyauta, ko kuma addini. A cikin roƙon baka ake faɗin maganganun da za su daɗaɗawa wanda ake yiwa roƙon rai, ko kuma su fifita shi bisa sauran jama’a wanda wannan ka iya motso shi ya yiwa maroƙin kyauta ta ban mamaki.

Ana yin roƙon baka ne a cikin jama’a, musamman a lokutan bukukuwanaure, suna, salla, da makamantansu. Mai yin wannan aiki shi ake kira maroƙi baki ko kuma ɗan ma’abba.

Haka nan kuma a wasu lokutan shi maroƙi kan bushi iska ya kintaci lokacin da ya ke zaton gwaninsa yana cikin nishaɗi ko yana tare da jama’arsa, sai ya je ya yi masa roƙo.

Manazarta:

gyara sashe

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.