Reem Freinah
Reem Omar Frainah ko wadda yawanci aka fi sani da Reem Frainah, ta kasance 'yar asalin Falastin ce, mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam.[1] Ita ce kuma Babban Darakta ta Ƙungiyar Aisha don kare Mata da Yara, wata ƙungiyar mata ta Falasdinu mai zaman kanta da ke aiki don cimma daidaituwa tsakanin mata da maza ta hanyar karfafa tattalin arziƙin da taimakon juna ga ƙungiyoyi a Zirin Gaza tare da mai da hankali kan Zirin Gaza da yankin Arewa .[1][2]
Reem Freinah | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | State of Palestine |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare hakkin mata da psychologist (en) |
Ita ce tsohuwar mai kula da shirye-shirye na kungiyar A'isha ta mata da kariyar yara lokacin da ta fara a zaman wata hukuma mai zaman kanta a shekarar 2009. A shekara ta 2011, ta kammala digirin-digirgir a cikin ilimin likitanci, daga baya ta zama Babban Darakta na AISHA. Mafi yawan ayyukanta sun haɗa da koyarwa, da kuma samar da ayyuka da yawa ga mata da Ƙananan yara dake fama da rikici a Gaza.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Aisha Association for Woman and Child Protection". aisha.ps.
- ↑ Frainah, Reem. "Palestinian Women Facing Odds". United Nations Office for the Coordination of Humanitarian Affairs.
- ↑ "Palestinian woman: defenseless before the law and the occupation -". pikara magazine (in Sifaniyanci). 2016-08-04.