Perpétue Nshimirimana (an haife ta a watan Fabrairu 1961) 'yar diplomasiyyar Burundi ce kuma marubuciya.

An haife ta a Bujumbura, Nshimirimana ta yi karatu a Lycée Clarté Notre Dame de Bujumbura kafin ta tafi Jami'a a Aljeriya, inda ta sami takardar shaidar difloma a aikin jarida daga Institut National des Sciences de l'Information et de la Communication. Ta koma gida a shekarar 1984 don yin aiki a gidan rediyon Television Nationale du Burundi. Ta yi aiki a matsayin mamba na majalisar ƙasa kan sadarwa da hukumar UNESCO ta ƙasa. Daga shekarun 1991 zuwa 1992 ta kasance mambar kwamitin tsarin mulki, kuma a shekarar 1993 ta yi aiki a hukumar zaɓe ta ƙasa. Bayan zaɓen Melchior Ndadaye a matsayin shugaban ƙasa, an naɗa Nshimirimana a matsayin wakiliyar dindindin na Burundi a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, rawar da ta kare da kisan Ndadaye daga baya a shekarar 1993. [1] Tun daga shekarar 2015 ta zauna a Switzerland. [2] A shekara ta 2005 ta sami lambar yabo ta "Femme exilée, Femme engages" saboda aikinta tare da marayun Burundi. [3]

An buga tarihin rayuwar Nshimirimana, Lettre à Isidore, a cikin shekarar 2004.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Perpétue Nshimirimana". Retrieved 25 November 2016.
  2. Ubwanditsi. "Lettre ouverte de Perpétue Nshimirimana à Bernard-Henri Lévy. - burundibwiza.com". Archived from the original on 29 July 2017. Retrieved 25 November 2016.
  3. "BURUNDI. Perpétue NSHIMIRIMANA lauréate du prix " Femme exilée, Femme engagée " - UMOYA". Retrieved 25 November 2016.