Parc des Princes (fassara turanci "Princes’ Park") filin wasan kwallon kafa ne dake a birnin Paris, kasar Faransa.[1] Mazauninta na nan ne a kudu maso yamma na babban birnin Faransa,[2] acikin 16th arrondissement na Paris, cikin Stade Jean-Bouin (rugby venue) kuma a tsakanin hanyar Stade Roland Garros (tennis venue).[1]

Filin wasan Kulub din PSG wato Parc des Princes, an kallo daga sama

Filin wasan, dake da adadin na Adadin mazauni guda 47,929 na yan'kallo,[3] itace filin wasan gida na Paris Saint-Germain tun daga 1974. Kafin bude Stade de France a 1998, kuma nan ne wurin wasan kungiyar football da rugby union.[4] filin Parc des Princes na zagaye ne da kusurwa hudu na mazauna da akafi sani da Présidentielle Francis Borelli, Auteuil, Paris da Boulogne Stands.[5] Mai zane Roger Taillibert & Siavash Teimouri suka tsara ginin fili, yanayin filin Parc des Princes na yanzu an bude shi ne a 4 June 1972,[6] akan kimanin kidi 80–150 million francs.[7] filin shine na uku da aka gina a yankin, an bude na farkon a 1897 da na biyun a 1932.[2]

PSG ta kafa tarihin samun yawan masu kwallo a 1983, da yawansu yakai 49,575 wanda suka kalli nasarar da kulub din ta samu na 2–0 akan Waterschei a UEFA Cup Winners' Cup quarter-finals.[8] Har wayau, French national rugby team yafi samun yawan masu kallo. A sanda ta doke Wales 31–12 a gasar 1989 Five Nations Championship a gaban masu kallo 50,370.[9]

ManazartaGyara

  1. 1.0 1.1 "PARC DES PRINCES". Paris2024. Retrieved 7 July 2016.
  2. 2.0 2.1 "Parc des Princes". UEFA.com. Retrieved 7 July 2016.
  3. "Parc des Princes". PSG.fr. Retrieved 19 July 2017.
  4. "The lowdown on the Parc des Princes". Real Madrid CF. 21 October 2015. Retrieved 7 July 2016.
  5. "Plan du Parc". PSG.fr. Retrieved 2 March 2017.
  6. "PSG firmly in the pantheon". FIFA.com. 17 October 2008. Retrieved 7 July 2016.
  7. "Le Parc des Princes". Info PSG. Retrieved 7 July 2016.
  8. "PSG-OM, record d'affluence au Parc des Princes en L1". Paris.canal-historique. 24 October 2016. Retrieved 23 November 2016.
  9. "Parc des Princes Paris". Stadium and Attendances. Retrieved 7 July 2016.