Owoidighe Ekpoatai (an haife ta a shekarar 1966) `yar siyasar Najeriya ce, `yar majalisa kuma memba a majalisar wakilai ta tarayya. Ta wakilci mazabar Eket/Onna/Esit Eket/Ibeno na jihar Akwa-Ibom.

Owoidighe ta yi karatun sakandare a makarantar sakandaren 'yan mata (GSS) AFANA kafin ta zarce zuwa Jami'ar Uyo, Uyo inda ta kammala digirin farko a fannin Accounting. A shekarar 2003, ta kammala digirinta na biyu a fannin kasuwanci (MBA) daga Jami'ar Jihar Imo, Owerri.

An zabe ta a Majalisar Dokoki ta kasa a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP.[1][2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "2015 House of Representative Election Results in Nigeria". whowin.com.ng. Retrieved 21 November 2020.[permanent dead link]
  2. Nigeria, Media (28 April 2018). "List Of Members Of The House Of Representatives Of Nigeria, 2015 – 2019". Media Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 16 August 2021. Retrieved 21 November 2020.