Oba Claudius Dosa Akran dan siyasan Najeriya ne kuma mai kambun gargajiya wanda ya wakilci Badagry a majalisa a 1951 kuma ya rike mukamin Aholu Jiwa II na Jegba. Ya kasance memba a kungiyar Action Group tun kafin samun yancin kai, sannan aka nada shi ministan kananan hukumomi da tsare-tsare na yankin a shekarar 1952. Ya kasance mai tasiri a jam’iyyar kuma ya kasance ministan kudi na yankin daga 1962 zuwa 1966.

An haifi Akran a shekara ta 1899 a gidan Kopon, wanda ya zama shugaban Jegba quarters na Badagry. Bisa ga umurnin wani limamin Katolika, mahaifinsa ya ba shi izinin zuwa makaranta, Akran ya halarci Kwalejin St Gregory, Obalende kuma ya kammala karatun sakandare a Kwalejin King. Ya yi aiki da Post and Telegraph Development na shekaru da dama, inda ya shiga sashen a shekarar 1926 ya tafi a 1947. Bayan rasuwar mahaifinsa a 1946, an zabe shi a matsayin shugaban Jegba quarters a 1948 kuma aka nada shi a 1950. A matsayin Oba. Akran na Badagry, ya kasance memba kuma daga baya shugaban karamar hukumar Badagry da kuma karamar hukumar Egun-Awori.

Akran ya yi tasiri wajen kafa makarantar Badagry Grammar a shekarar 1955, makarantar sakandare ta farko a Badagry da sauran ci gaban ababen more rayuwa a Badagry kamar post da telegraph, kayan lantarki da hanyoyin mota.

Manazarta

gyara sashe

[1] [2]

  1. Ogunremi, Gabriel Ogundeji; Opeloye, M. O.; Oyeweso, Siyan (1994). Badagry: A Study in History, Culture and Traditions of an Ancient City. Rex Charles Publications. pp. 344–350. ISBN 9789782137241.
  2. Podo, Sunday (March 10, 2018). "Oba Akran: The legend who combined politics, tradition"