Nusaiba Shuaibu Ahmad (An haifi Nusaiba a shekara ta dubu biyu 2000 a jahar Kano) kuma tana da miji. Ita ce gwarzuwar musabaƙar Alƙur'ani to shekarar 2021 da aka yi a garin Kano.

Gwarzuwar musabaƙar shekara ta 2021 ta haddace Ƙur'ani tun tana 'yar shekara 15 bayan ta fara haddar littafin mai tsarki tana 'yar 11 zuwa 12, kamar yadda ta shaida wa BBC.[1]

Karatu gyara sashe

Ta kammala sakandare, inda yanzu haka take zuwa jami'a.

Gasa gyara sashe

Nusaiba Shuaibu Ahmad ta fara shiga gasar karatu wato musabaƙa a shekarar 2017, Daga cikin nasarorin da ta samu, ta taɓa zama gwarzuwar musabaƙa wadda cibiyar Alfijir ke shiryawa a Kano, Kazalika ta taba zuwa ta biyar a musabaƙar ƙasa, wadda aka gudanar a Jihar Katsina, Suratul Jinn - sura ta 72 - ita ce ta fi bai wa makaranciyar wahala a loƙacin da take hadda. "Saboda tana da ayoyi masu kama da juna," in ji ta.

Manazarta gyara sashe

  1. BBC Hausa. "Gwarzuwar Gasar al-Qurani 2021". Retrieved 28 March 2021.