Nuhu Poloma
Nuhu Poloma (An haifeshi ranar 2 ga watan Satumban shekarar 1941) a Gelengu, Jihar Bauchi, Najeriya. Ya kasance ɗan siyasa mai kishin ƙasa kuma mahaifin fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu. Ya kasance shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe kafin ya rasu.[1][2] Ali Nuhu
Tarihin rayuwa
gyara sasheYa kasance na biyu da haihuwa a gurin mahaifinsa Malam Yarda Poloma. Poloma malami ne a Gelengu da ke jihar Gombe yayin da mahaifiyarsa Madam Sindaba Poloma ce. Ya auri Mrs. Ansa Poloma (nee Obong) kuma aurensu ya albarkaci ‘ya’ya hudu – Ali Nuhu, Kabiru Nuhu, Sama'ila
Nuhu ya yi karatun firamare da sakandire a makarantar SIM dake Gelengu, jihar Gombe, daga shekarar 1951 – 1958. Daga nan ya wuce makarantar P. £r T. Kaduna inda ya samu shaidar horar da ‘yan kasa (Territorial Training Certificate) bayan ya yi karatu na tsawon shekaru 2, daga 1960 – 1962. Ya kasance a Federal Training Centre (FTC) Kaduna daga shekarar 1963 zuwa 1964 kuma ya sami takardar shedar karatun sakatariya. Domin neman takardar shedar karatun boko, Nuhu ya kawar da yakin basasar Najeriya a lokacin da ya tafi kasar Amurka domin ci gaba da karatunsa. Ya kammala karatunsa a shekarar 1975 a Kwalejin Kwastam da ke Washington D.C, Amurka, kuma ya sami shaidar difloma a fannin Kwastam da Leken Asiri na ƙasa da ƙasa.
Ayyuka
gyara sasheHon. Poloma ya dawo Najeriya ya shiga hukumar kwastam ta Najeriya. Ya samu karin girma zuwa babban mataimaki na kwastam a shekarar 1976. Lokacin da ya bar hukumar kwastam ta Najeriya, aka nada shi Daraktan Kamfanin Yankari Dallas Limited inda ya yi aiki daga 1976 zuwa 1979. Ya kasance dan majalisar wakilai ta Tangale-Waja ta Arewa, Bauchi. Jiha a ƙarƙashin jam'iyar NPN a shekarun 1979-1983.
Mutuwa
gyara sasheHon. Nuhu Poloma ya rasu ne a ranar 8 ga watan Yunin, shekara ta 2020.[3]