Nakedi Lekganyane
Nakedi Maria Lekganyane ’yar siyasar Afirka ta Kudu ce wacce ta wakilci jam’iyyar ANC a majalisar dokokin lardin Limpopo tun daga shekarar 2019. An zaɓe ta a kujerarta a babban zaɓen shekarar 2019, inda ta zo ta goma a jerin jam'iyyar ANC. [1]
Nakedi Lekganyane | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a |
Lekganyane a da ta wakilci ANC a matsayin kansila a gundumar Capricorn. An fara zaɓan ta a cikin Kwamitin Magajin Garin Capricorn a shekarar 2010 [2] kuma an zaɓe ta a matsayin Kakakin majalisar bayan zaɓen ƙananan hukumomi na shekara ta 2016, tana aiki a ƙarƙashin magajin gari John Mpe. [3] Ta yi murabus daga majalisar bayan zaɓen ta 2019 kuma Monica Mohale ta gaje ta a matsayin kakakin majalisar. [4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Nakedi Maria Lekganyane". People's Assembly (in Turanci). Retrieved 2023-01-24.
- ↑ "Farewell to two CDM stalwarts". Polokwane Observer (in Turanci). 2019-07-04. Retrieved 2023-01-24.
- ↑ "Capricorn District Municipality Mayor sworn in". EWN (in Turanci). 26 August 2016. Retrieved 2023-01-24.
- ↑ "Mohale elected as new CDM Speaker". Polokwane Observer (in Turanci). 2019-05-30. Retrieved 2023-01-24.