Musa Bello (An haife shi a shekarar alif 1919 - Ya rasu a shekara ta alif 1975) shi ne Etsu Nupe na 11 a masarautar Nupe ya yi sarauta daga shekarar alif 1967 zuwa rasuwarsa a shekara ta alif 1975 sannan Etsu Nupe Umaru Sanda Ndayako na 12 ya gaje shi.

Musa Bello
Rayuwa
Haihuwa 1919
Mutuwa 1975
Sana'a

Tarihi gyara sashe

Mahaifinsa, Bello Maliki, shi ne na bakwai Etsu Nupe. Ya yi karatunsa gaba daya a masarautar Bida sannan daga baya ya zama babban hakimin Badeggi a shekara 1965 da Katcha kafin daga nan ya yi aiki a kamfanin kwangila na Kaduna. Ya kasance daga gidan sarautar Masaba a Masarautar Nupe da Bida. Kaka ne ga Etsu Nupe Yahaya Abubakar na 13 a yanzu, kuma kawu ne ga Etsu Nupe Umaru Sanda Ndayako na 12 duk sun zo cikin gidan sarauta daban amma kakansu ɗaya wato Malam Dendo.

Manazarta gyara sashe

https://allafrica.com/stories/200309100284.html https://www.dailytrust.com.ng/meet-the-royal-ndayakos-of-bida-262995.html Archived 2020-04-28 at the Wayback Machine