Muhammadu Attahiru Dan Aliyu Babba (an haife shi a shekara ta alif 1903 – 1915) Shekarun 19th da kuma 20th, sun kuma kasance masu rudani ga tarihin Kalifancin Sokoto. A wannan lokutan Kalifofi sun fuskanci matsaloli dayawa musanman daga turawan mulkin mallaka.[1]

Muhammadu Attahiru Dan Aliyu Babba

Attahiru na II biyu yayi karatu a karkashi mahaifinsa inda daga bisani ya koma karkashin sauran malamai. Shekarar shi hamsin da takwas (58) lokacin da turawa suka amince a nada shi a matsayin sabon sultan.[2]

Bayan yakar Sokoto da turawa sukayi Lord Lugard ya tafi garin Sokoto inda Waziri Buhari bayan hijiran Kalifa Attahiru na daya (I). Ya kuma rubutawa Lord Lugard sako cewa za suyi mubayi’a shida sauran manyan Masarautar Sokoto. Yace danago naji baza su, hanamu sallah ba, ba su hana mu zakka ba kuma basu doge sai munbi addininsu ba sai na zauna dasu nayi aiki dasu. Turawa sun goyi bayan nada Attahiru na biyu. A matsayin sabon Sarkin Musulmi. Bayan an nemi Attahiru na farko ba’a ganshi ba kuma ba mai labarin sa, sai aka nada Attahiru na biyu da yardar Lord Lugard a ranar 21st ga watan Maris ɗin shekara ta alif 1903.[2]

Mutuwar Sultan Attahiru na biyu II, ya kawo karshen wani babi a tahirin Kalifancin Sokoto ya kafa tarihin zama na farko wanda yayi aiki karkashin kulawan turawa kuma yayi nasara. Duk da matsi da kuma hali na takura daga turawan, inda wasu dayawa daga cikin Sarakuna basu dade ba kamar yadda shi yayi kuma yaci nasara.[2]

  • Bobboyi, H., Yakubu, Mahmud.(2006). The Sokoto Caliphate: history and legacies, 1804-2004, 1st Ed. Kaduna, Nigeria:Arewa House. ISBN 978-135-166-7
  • Hamman, Mahmoud, 1950- (2007). The Middle Benue region and the Sokoto Jihad, 1812-1869 : the impact of the establishment of the Emirate of Muri. Kaduna: Arewa House, Ahmadu Bello University. ISBN 978-125-085-2. OCLC 238787986.
  • Usman Muhammad Bugaje. The Tradition of Tajdeed in West Africa: An Overview International Seminar on Intellectual Tradition in the Sokoto Caliphate & Borno. Center for Islamic Studies, University of Sokoto (June 1987)
  • Hugh A.S. Johnston . Fulani Empire of Sokoto. Oxford: 1967. ISBN 0-19-215428-1.
  • S. J. Hogben and A. H. M. Kirk-Greene, The Emirates of Northern Nigeria, Oxford: 1966.
  • Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN 978-978-956-924-3. OCLC 993295033.

Manazarta

gyara sashe
  1. Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. p.p-215-243 ISBN 978-978-956-924-3.
  2. 2.0 2.1 2.2 Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. p.p 245-261 ISBN 978-978-956-924-3.