Muhammadu Bashar

hoton muhamad bashar
Sarkin Daura Alhaji Dr. Muhammadu Bashar riƙe da Sandar Mulki
Sarkin Daura Alhaji Dr. Muhammadu Bashar riƙe da Sandar Mulki

Saraurata

gyara sashe

Muhammadu BAshar shi ne wanda yagaji kakansa Alhaji Abdurrahnam a cikin watan Yuni na shekara ta 1966. Zamanin sarki Muhammadu Bashar, zamani ne na canje-canje masu dimbin yawa. A wajn sha'anin mulki, an sami babban canjin tsarin mulki irin na En'e (NA)ya kau, an kuma maye gurbinsa da tsarin ƙaramar hukuma. Gidajen Shari'ah da Alƙalai suka koma hannun gwamnati. An kuma mayar da 'yan doka da gandurobobi daga hannun ƙaramar hukuma zuwa hannu gwamnatin tarayya. ilmin zamani ya haɓaka da gaske. An buɗe makarantu iri iri da yawa. Abubuwan zamani na jin dadin sun samu a ƙasar Daura. Hanyoyi masu kyau sun samu, An sanya wutar lantarki. An buɗe asibitocin Daura da Baure. An kuma faɗaɗa da kyautata garin Daura da sauran garuruwan hakimai.

A cikin shekarar 1982, aka ɗaukaka sarautar Daura daga daraja ta biyu zuwa daraja ta ɗaya. Haka kuma a shekara ta 1988 aka raba ƙaramar hukumar Daura zuwa ƙananan hukumomi biyu , wadanda su ne karamar hukumar Daura da Zango . A shekara ta 1991 aka ƙara ƙaramar hukumar Mai'adua. Daura ta zama ƙaramar hukuma 5 a cikin shekarar 1992 saboda karo Sandamu da Baure. A wannan shekarar ne kuwa aka raba ƙasar Sarkin Daura daga hakimai biyar zuwa Hakimai Goma. A lokacin da mai martaba Dr. Muhammadu Bashar ya hau kan sarauta a shekarar 1966 an kuma sami ƙaruwar ruwan sha, kiwon lafiya, aikin gona, hanyoyin mota, wutar lantarki, kasuwanci, noman rani, linkin balinki.[1] Sarki mai sha'awar ilimin zamani ne na a saboda haka ya nema ya matukar kokarin kawo wayewar kan jama'arsa na yin rangadin makarantu na ƙasarsa. Misali akan makarantun Primary guda 8 ne a ƙasar Daura a lokacin da ya hau kan mulki amma a lokacin shi ƙasar Dauta tana da makarantun primary sama da Dari uku 300.

Abinda mai martaba Sarkin Daura yayi wa ƙasarsa sai dai Allah yayi masa sakaiyya.[2] Saboda himma da kwazansa, Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Muhammadu Bashar ya sami lambobin na girmamawa kamar haka:

Lambobin Yabo

gyara sashe
 
Muhammadu Bashar

1. OBE a 1960 saboda kwazansa na yako kamaru ta Arewa zuwa Najeriya wadda itace lardin Sardauna a da, yanzu itace Adamawa da bangaren Jihohin Taraba da Barno. 2.OFR a 1964 wadda gwamnatin Sir Abubakar Tafawa Balewa ta bashi. 3. 1982 Sarki mai MArtaba da Daraja ta ɗaya daga Gweamnatin Abba Musa Rimi Jihar Kaduna. 4. OSR 1988 Mutum mai daraja ta daya wadda Gwamnatin Niger Republic ta ba shi. 5. CON 2003 wadda gwamnatin Olesuegu Obasanjo ta Bashi. Mutanen Daura suna Alfahari da rayuwarsa domin irin cigaba da ak samu a lokacinsa wadda ba'a sami saurin ci gaba ba tun daga lokacin magajiya Daurama.

Yayi mulkin Masarautar Daura cikin Shekaru 41 cikin NAsara tun daga shekara ta 1966 har Allah ya karɓi ransa a watan Fabarairu na shekara ta 2007. Allah ji kan Alhaji Dr. Muhammadu Bashar da Rahma.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2023-03-09. Retrieved 2023-03-11.
  2. https://en.wikipedia.org/wiki/Daura_Emirate
  3. https://en.wikipedia.org/wiki/Daura_Emirate