Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha

Lamiɗon Adamawa Alhaji Muhammadu Barkinɗo Aliyu Mustafa (An haife shi a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 1944) a garin Yola dake jihar Adamawa ta yanzu.[1]

Alhaji Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha (Lamiɗon Adamawa)

Karatu gyara sashe

Ya fara karatun sa na Firamare ne a Mubi daga shekakar 1951 zuwa 1954. Bayan nan kuma ya halarci makarantar middle ta Yola a shekakar 1955.[2]

Bayan da ya kammala karatu a makarantar middle a shekarar 1957, ya halarci makarantar Firamare ta kwana dake Dutsen-Ma daga shekarar 1958 zuwa 59. kafin ya halarci sakandaren Zariya a shekakar 1960.[3]

A shekarar 1965 ya halarci kwalejin Barewa dake Zariya daga nan ne kuma ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariyan, inda kuma ya samun shedar Diploma a harkokin shari'a daga shekarar 1967 zuwa 1969.[4]

Kwasa-kwasai Lamiɗon wanda keda takardar shedar Digirgir ta Dr ya halarci Jami'ar Saint Clement University dake West Indies a Birtaniya da kuma wasu kwasakwasan a nan Jamus inda ya ƙware a harkokin sufurin Jiragen ruwa.

Aiki gyara sashe

Tsakanin shekarun 1979 zuwa 1983 sabon lamiɗon ya zama kwamishinan aiyuka da lafiyan dabbobi na shekaru huɗu. Daga shekarar 1991 zuwa 2003 kuma Maimartaba Lamido yayi aiki da hukumar matatan manfetur ta ƙasa, ya kuma zama shugaban kamfanin gine-ginen hanyoyi ta Sterling dake kaduna. Kafin daga bisani ya zama shugaban hukumar gidan Radiyon Tarayya ta FRCN. Haka kuma yayi aiki a matsayin jami'in kwastan.

Sarauta gyara sashe

Ranar Asabar 19 ga watan Yuni, shekara ta 2010, gwamnan jihar Adamawa a tarayyar Nigeria Admiral Murtala Nyako GCON, (Sarkin yamman Adamawa), ya jagoranci bikin ba da sanda ga sabon Lamidon Adamawa na 12; Alhaji Dr. Muhd. Barkindo Aliyu Mustapha. Mataimakin shugaban tarayyar Nigeria Arc. Namadi Namadi Sambo, da Mai alfarma Sarkin musulmi Dr. Muhd. Sa’ad Abubakar na uku mni, tare da kusan daukacin sarakuna daga dukkan sassan kasar sun halarci taron.

Manazarta gyara sashe