Muhammad Uba Gurjiya (An haife shi a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da biyu 1982) a garin Gurjiya dake karamar hukumar Bunkure.

Ya yi karatun firamare a makarantar Gurjiya Central Primary School, Bunkure Junior Secondary School 1994-1996 da Senior Secondary School a Famous School for Arabic Studies (SAS) Kano tsakanin 1997-2000 bi da bi.[1] A tsakanin 2000-2003 ya halarci Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano inda ya yi kwas dinsa na NCE da Jami'ar Bayero ta Kano (2006-2010) inda ya yi digirinsa na ilimi.

Aiki da Siyasa

gyara sashe

Ya rike kwamitoci da dama ciki har da na Kudi Ya shiga aikin hukumar kula da ilimi ta kasa (SUBEB) kuma ya kasance jami'in cibiya ta karamar hukumar Bunkure tsawon shekaru 4. ya taba zama malamin makaranta kafin ya shiga siyasa.

A shekarar 2015 Aka zaɓe shi don wakiltar'karamar Hukumar Bunkure a Majalisar Jiha 2015-2019. Sannan akaro na biyu ya kuma lashe zaben sa a shekarar 2019.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. http://avarinlogspot.blogspot.com/2020/02/kano-assembly-removes-majority-leader.html?m=1
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-11-07. Retrieved 2021-11-07.