Muhammed Salihu Audu wanda aka fi sani da Muhammed S. Audu masani ne ɗan Najeriya. Ya yi aiki a matsayin Shugaba (Vice-chancellor) na shida a Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna daga shekarun 2007 zuwa 2012.[1][2] A halin yanzu shine mataimakin shugaban (Vice-chancellor) na jami'ar tarayya dake Lokoja.[3][4]

Muhammad S. Audu
Rayuwa
Haihuwa Jihar Kogi
Karatu
Makaranta Jami'ar Usmanu Danfodiyo Bachelor of Arts (en) Fassara
Jami'ar Bayero Master of Arts (en) Fassara
Jami'ar jihar Benuwai Doctor of Philosophy (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Malami
Employers Federal University of Technology, Minna  (2007 -  2012)
Federal University Lokoja  (2021 -

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haifi Mohammed Salihu Audu ga Sule da Salamatu Atta Audu, wadanda ’yan asalin Ebira ne. Ya fara karatun firamare a makarantar firamare ta Katolika ta RCM da ke Okene da kuma St. William Primary School, Ilorin. Ya cigaba da karatunsa na sakandire a Community Secondary School Okene da Ansarul Islam dake Ilorin. Ya kammala karatunsa a Jami'ar Usman Danfodio Sokoto inda ya samu digiri (B.A) a tarihi, sannan ya ci gaba da karatun digirinsa na M.A. a fannin hulda da kasa da kasa a Jami'ar Bayero ta Kano sannan ya yi digirinsa na uku a Jami'ar Benue da ke Makurdi.[3]

Mohammed Audu ya yi aiki a matsayin malami, mai bincike kuma ƙwararren ɗan takarar ci gaban al'umma ne. Farfesa ne a fannin Tarihi da Nazarin Duniya kuma a halin yanzu Mataimakin Shugaban Jami'ar Tarayya ta Lokoja.[4]

Ya wallafa mujallu na ilimi da litattafai da yawa musamman Yaki da Zaman Lafiya a Karni na 20 da Jama'ar Najeriya da Al'adu.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. Offiong, Adie Vanessa (7 March 2013). "Nigeria: Basic Education Is Problematic - Don". Daily Trust. Abuja – via AllAfrica.
  2. Jimoh, Yekini (14 November 2020). "Kogi Inaugurates Implementation Committee On 'Confluence University Of Science & Technology'". Nigerian Tribune. Lokoja. Retrieved 25 February 2022.
  3. 3.0 3.1 3.2 "Muhammed Salihu Audu | Staff Profile". Federal University Lokoja. Retrieved 25 February 2022.
  4. 4.0 4.1 Dende (25 March 2021). "FULokoja senate appoints Prof. M. S. Audu as deputy Vice Chancellor". My School News. Retrieved 25 February 2022.