Muhammad Ballo (An haife shi ranar 6 ga watan Yuni, shekara ta 1966), a garin Butu–Butu

Karatu gyara sashe

Ya halarci makarantar firamare ta Butu – Butu a tsakanin shekarar 1974 – 1980. Ya yi Karamar Sakandare a Dawakin Tofa tsakanin shekarar 1980 – 1983 yayin da babbar sakandaren sa ke Bagauda Technical tsakanin shekarar 1983 – 1986. Daga shekara ta 1986 – 1990 ya kasance a Makarantar Fasaha ta Kano don samun shaidar karatunsa ta kasa (NCE), tare da nuna sha'awa a fannin fasaha tsakanin shekarar 1992 – 1995, Hon. Butu – Butu ya halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna inda ya yi digirin sa na farko na ilimi (Technical). Difloma a fannin gudanarwa da kimantawa, Jami'ar Bayero, Kano.

Aiki da Siyasa gyara sashe

Ya yi aiki a ma’aikatar ilimi daga shekarar 1990 zuwa 2014. Ya kasance malamin makaranta, jami’in jarrabawa, Babban Jagora (Academic and Administration). [1] Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban makaranta da babban jami’in ilimi (C.E.O), sa ido da tantancewa. A cikin gogewarsa ta siyasa. An nada Bello a matsayin kansila mai kula da harkokin ilimi da ci gaban al’umma. Ya taɓa zama Mataimakin Shugaban Rimin Gado. An nada shi Babban Mashawarci na Musamman Ma'aikatar Lafiya a shekarar 2000 - 2003 da Jami'in Gudanarwa na wucin gadi (IMO) shekarar 2011 - 2014. [2]

Sannan yazama ɗan majalisar jaha dake wakiltar Rimin Gado da Tofa 2015- 2019 kuma shine shugaban masu Rinjaye na majalisar.

Ya sake Lashe zaɓe a karo na biyu a shekarar 2019 Duk a karkashin Jam'iyyar APC, wanda yanzu haka yana rike da mukamin shugaban kwamitin ilimi na majalisar jahar kano.

Manazarta gyara sashe