Sanin kowa ne cewa kifi ba ya da wani takamammen muhalli da yake rayuwa wanda ya shige ruwa. Don haka harkar Sarkanci akan gudanar da ita ne a cikin ruwa. Dalilin haka ba abin mamaki ba ne ya kasance an sami wani rukuni na Basarken Karin Magana wanda ya jiɓinci ruwa. Misalai na Basarken Karin Magana masu magana a kan ruwa shi ne:

Gurin rayuwan kifi

v Ruwan da suka ci ka su ne ruwa

v Ba a cinikin kifi a ruwa.

v A wanki kifi da ruwansa

v Idan kana ruwa kada ka zagi kada.

v Ƙaryar rijiya ruwa na gulbi.

v Gwanin ruwa shi ruwa kan ci.

v Ruwa ya ƙare wa ɗan kada bai gama wanka ba.

v Ta- da- ta, wankin ɗankanoma mashaya.

v Iya ruwa fid da kai

v Ruwa na Allah kifi ma na Allah.

v A rabe da alwalar kifi a ruwa.

v Ratsa ruwa ba a sha ba, ba ya maganin ƙishirwa.

v Kifin rijiya.

v Su ya kai gurbi.

v Shirin shiga ruwa tun tudu ake yinsa.

v Shiru kamar ruwa ya ci su.

v Duk yadda tsari ya san ruwa kada ya fi shi.[22]

Idan aka dubi wannan rukuni na Basarken Karin Magana za a fahimci cewa kowane misali daga ciki yana magana ne a kan ruwa. Akwai zancen ruwa na gulbi mai yawan gaske wanda ba a iya kwatanta shi da na rijiya wanda yake ɗan kaɗan,

da kuma nuna aikin iyo da fito a ruwa wanda aiki ne da kacokam da ya rataya a wuyan Sarkawa ta hanyar amfani da kwalekwale ko gora. Haka ma akwai zancen wasu halittu da ake samu a ruwa waɗanda ke zaune a muhalli ɗaya da kifi can cikin ruwa kamar kada. Rukunin na Basarken Karin Magana ya yi tsokaci kan amfani da ruwa kamar yadda aka saba a al’ada wanda kan haɗa da sha domin maganin ƙishirwa da wanka domin gusar da datti.