Mu'azu ibn muhammad bello
Mu'azu Ibn Muhammad Bello Kalifa Mu’azu jika ne ga Shehu Dan Fodio daga wajen Muhammadu Bello. Daga ɓangaren uwa kuma jika ne na aminin Shehu Bin Fodio Umar Mu’alkamu. Ya kasance wanda ya kawo zaman lafiya a lokacin sa.
Tarihin rayuwar
gyara sasheAn kuma haife shi a shekarar 1814 kuma yayi mulkin na tsawon shekara 4. Ya kasance jika ga Shehu kuma jika ga aminin Shehu.[1]
Al-Ajabi
gyara sasheYa kuma kasance yana zama tare da Shehu kakansa tun yana shekara hudu shida dan uwansa wato kaninsa. Inda Shehu ke kiransu dashi Mu’azu da Lamido, shi kuma dan uwansa Sa’id da Modibbo. An rawaito cewa Shehu na musu addu’ar Allah ya ba dayansu ilimin, shi kuma Allah yaba daya mulki. Inda Allah ya amshi addu’ar Shehu inda Mu’azu ya zama Kalifa sannan Sa’id ya zama shahararren malami.
Karatu
gyara sasheKalifa Mu’azu ya kasance mai ilimi, wannan ya samo asali ne ga asalin iyayenshi. Ya kuma yi makarantar Al-Qur’ani tun yana yaronsa, a wajen mahaifinsa. Inda daga baya yayi sauran karatu a wajen malamain cikin garin su.
Sarauta
gyara sasheKalifa Abubakar Atiku Ibn Bello ya rasu a march 1877, hakan yasa kujerar babu kowa. Mu’azu Lamido da Modibbo Sa’idu sun nema kujerar hakan yasa akabi tsari na zabar sarki, inda shi Mu’azu Lamido Allah ya bashi sarautar duba da wasu dalilai na ilimi da kuma kwarewa akan mulki. An nada shi Kalifa a ranar Alhamis 3rd April 1877 a Wurno Central Mosque.[1]
Rasuwa
gyara sasheKalifa Mu’azu yayi mulki na tsawon shekara hudu (4) da wata tara (9) daga 1877 – 1881. Ya rasu a ranar Litinin 26th september 1881. A lokacin yana da skekara 68, an binne shi a Sokoto a makabartar kakanshi. Wacce ake kira ‘Hubbaron Shehu’.[1]
Bibiliyo
gyara sashe- Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN 978-978-956-924-3. OCLC 993295033.
- The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.
- Smaldone, Joseph P. (1977). Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710