Dutsen Kailash
Dutsen Kailash[1] dutse ne a gundumar Ngari, yankin Tibet mai cin gashin kansa na kasar Sin. Ya ta'allaka ne a cikin Kewayen Kailash (Tunukan Gangdisê) na Transhimalaya, a yammacin Tibet Plateau. Dutsen Kailash bai wuce nisan kilomita 100 (mil 62) arewa da yankin yammacin iyakar China, Indiya, da Nepal.[2]
Dutsen Kailash | |
---|---|
General information | |
Height above mean sea level (en) | 6,638 m |
Topographic prominence (en) | 1,319 m |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 31°04′01″N 81°18′46″E / 31.0669°N 81.3128°E |
Mountain system (en) | Gangdise Shan (en) |
Kasa | Sin |
Territory | Ngari Prefecture (en) |
Dutsen Kailash yana kusa da tafkin Manasarova da tafkin Rakshastal. Tushen manyan koguna huɗu na Asiya suna kusa da wannan dutsen da tafkunan biyu. Waɗannan kogunan su ne Indus, Sutlej, Brahmaputra, da Karnali (wani rafi na Ganges, wanda Mabja Zangbo ke ciyar da shi). Ana ɗaukar Dutsen Kailash mai tsarki a cikin addinai huɗu: Hindu, Buddha, Jainism da Bon.[3][4]
Yawancin mahajjata daga Indiya, Tibet, Nepal, da sauran ƙasashe suna tafiya don girmama dutsen.[5]
Nazari
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2014-12-28. Retrieved 2023-12-31.
- ↑ https://www.kailash-yatra.org/kailash-mansarovar-yatra-via-nathula-pass-sikkim.html
- ↑ https://kathmandupost.com/money/2018/05/16/kailash-manasarovar-yatra-likely-to-see-record-numbers
- ↑ https://www.suunto.com/sports/News-Articles-container-page/Kailash-the-mountain-that-calls/
- ↑ https://www.kailash-yatra.org/kailash-mansarovar-yatra-via-nathula-pass-sikkim.html