Mohamed Tissir (an haife shi a shekara ta 1976) ɗan wasan dara ne na ƙasar Morocco.[1]

Mohamed Tissir
Rayuwa
Haihuwa 27 Nuwamba, 1976 (47 shekaru)
ƙasa Moroko
Harshen uwa Abzinanci
Karatu
Harsuna Larabci
Abzinanci
Sana'a
Sana'a chess player (en) Fassara

Sana'a/Aikin Chess

gyara sashe

Ya lashe gasar Chess ta Afirka a shekarar 1999, gasar Chess ta Morocco a 1996, 1999 da 2005, kuma ya wakilci kasarsa a wasannin Chess da dama. Ya kuma ci lambar zinare a gasar Chess Olympiad na Palma de Mallorca (Spain) na 36 a shekara ta 2004 sannan kuma ya lashe wasannin Larabawa da aka gudanar a ƙasar Jordan a shekarar 1999.

Ya taka leda a gasar cin kofin duniya ta Chess a shekara ta 2000, inda ya kare a ƙasan rukunin D, da kuma FIDE World Chess Championship 2004, inda Alexey Dreev ya doke shi a zagayen farko.[2]

Shi ma kocin wasan dara ne.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Tissir vs. Dreev, Tripoli 2004". Chessgames.com.
  2. "Tissir vs. Dreev, Tripoli 2004". Chessgames.com.

"Tissir vs. Dreev, Tripoli 2004". Chessgames.com.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe
  • Mohamed Tissir rating card at FIDE
  • Mohamed Tissir chess games at 365Chess.com
  • Mohamed Tissir player profile and games at Chessgames.com
  • Mohamed Tissir's profile in lichess.org
  • Mohamed Tissir's profile in chess.com