Mohamed Hamdy Zaky wanda aka fi sani da Mohamed Hamdy kwararre ɗan wasan kwallon kafa ne na ƙasar Masar, wanda ke taka leda a kulob din Ismaily na Masar a gasar Premier ta Masar, a matsayin dan wasan gaba.[1]

Tarihinsa na kwallon kafa

gyara sashe

Hamdy ya taka leda da Masar U20 a gasar cin kofin duniya ta FIFA U-20 na 2011.[2]Hamdy ya fara buga wasansa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Masar a ranar 8 ga Yuni, 2015, da Malawi.[1] [2]