Yana daya daga cikin kalolin miyar gargajiya na hausa

Yanda akeyin miyar gyara sashe

Kayan hadi

_Tattasai

_Attarugu

_Albasa

_Tafasa

_Maggie

_Gishiri

_Garlic thyme

_Seasoning spices

_Nama

_Kifi busashshe

_Man ja or man gyada

_Gyada

Yanda ake hadaqa

_Za’a tafasa nama a sanya thyme da maggie da albasa bayan ya tafasa sai a sanya mai a tukunya ki soyashi da albasa saiki zuba kayan miyarki ki kuma sanya naman da kika tafasa tare da ruwan da kika tafasa naman saiki zuwa gyadar ki wadda kin riga kin gyarata kin daka ta da busashshen kifin ki shima bayan ki gyara abunki saiki sanya curry da maggie gishiri saiki barshi yayi kamar 10mnts saiki zuba tafasan ki bayan kin gyarashi anaso ki zuba zogalen da yawa domin anfiso miyar tayi kauri saiki barshi kan wuta yayi kamar  15mnt shikenan saiki sauke_