Mesut Ozil

Dan kwallon kafa na kasar Jamus

Mesut Özil (furucci|ˈmeːzut ˈøːzil, ko |meˈsut ˈøzil|; An haife shi a ranar 15 ga watan October shekara ta alif 1988).kwararren dan kwallon kafa na ƙasar Jamus ne, wanda ke buga wasa a kulob din fenerbahce F.C Wanda akewa lakani da suna the assist king Ana kuma ganin yana daga cikin gogaggun yan'wasa a duniya.[1][2][3]

Mesut Ozil
Rayuwa
Haihuwa Gelsenkirchen, 15 Oktoba 1988 (35 shekaru)
ƙasa Jamus
Turkiyya
Ƙabila Turks in Germany (en) Fassara
Turks (en) Fassara
Ƴan uwa
Abokiyar zama Amine Gülse  (7 ga Yuni, 2019 -
Ma'aurata Amine Gülse
Mandy Capristo (en) Fassara
Mandy Capristo (en) Fassara
Mandy Capristo (en) Fassara
Karatu
Harsuna Jamusanci
Turkanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Rot-Weiss Essen (en) Fassara-
  FC Schalke 04 (en) Fassara2006-2008300
  Germany national under-19 football team (en) Fassara2006-2007114
  Germany national under-21 football team (en) Fassara2007-2009165
  SV Werder Bremen (en) Fassara2008-20107113
Real Madrid CF2009-201310527
  Germany national association football team (en) Fassara2009-20189223
Arsenal FC2013-24 ga Janairu, 202118433
Fenerbahçe Istanbul (en) Fassara24 ga Janairu, 2021-ga Yuli, 2022328
İstanbul Başakşehir F.K. (en) Fassaraga Yuli, 2022-22 ga Maris, 202340
 
Muƙami ko ƙwarewa attacking midfielder (en) Fassara
Nauyi 76 kg
Tsayi 1.8 m
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm3932946
mesutoezil.com
Ozil da boteng a Germany
File:20180602 FIFA Friendly Match Austria vs Germany Mesut Özil 850 1040.jpg
Ozil a cikin filin wasa
Ozil tare da alonso a team din real Madrid
Ozil Yayin da yake bugawa real Madrid
Ozil Yayin wasa
Ozil Yayin training
mesut Ozil a cikin kayan gida
Ozil a team din arsenal
Ozil tare da seedorf

tarihin kwallonsa gyara sashe

Özil na buga wasa yawanci a matsayin dan wasa nagaba amma a tsakiya, kuma ana sanya shi buga wasa a matsayin gefe (winger). Ya kuma fara wasan sa na kwararru a matsayin dan'wasan kulob din garin su Schalke 04 a gasar Bundesliga, inda ya share kaka biyu sannan ya koma Werder Bremen da kudin sayan sa €5 miliyan Ya samu cikakken karbuwa da mayar da hankali akan sa a gasar cin kofin duniya wato '2010 FIFA World Cup', sanda yake da shekaru 22, Özil ya taka rawar gani sosai a kungiyar sa da suka kai matakin gab da na karshe wato semi-finals, inda kuma suka yi rashin nasara a hannun wadanda suka lashe gasar Spain. An tsaida Özil a cikin takarar wadanda za,aba kyautar Golden Ball Award, sannan an bashi matsayin wanda yafi kowa yawan taimako acin kwallaye (assists) a cikin manyan gasar kasashen Turai da Ƙananan gasanni, wanda yake da 25.[4] Hakan yasa ya kara daraja inda aka saye shi akan kudi €15 miiyan zuwa gasar La Liga wanda kulob din Real Madrid F.C.suka sayeshi a matsayin Dan wasa

A kulob din Real Madrid, Özil ya samu lashe Copa del Rey a kakan sa na farko, sannan yayi taimako wajen bada gudunmawa na cin kwallaye guda 17 (assists) wanda kulob ta lashe gasar sifaniya kakan wasa bana.[5] Ya kuma lashe Supercopa de España a wannan kakar, inda yayi suna akan 'his technical skills and creativity; saboda iya aiki da karfin hali atsayin sa na attacking midfielder, shi yasa ake dan ganta shi da Zinedine Zidane daga tsohon mai hordashi shi José Mourinho.[6]

Bayan kulob din sa sun Kare a matsayi na biyu a La Liga bayan kulub din Barcelona ta lashe gasar shekarar 2012–13 kakar, Özil ya koma kasar ingila Dan buga wa kulob gasar firimiya a Arsenal da kudin da kulub din bata taba kashewa wani dan'wasa ba £42.5 miliyan (€50 miliyan),[7] haka yasa ya zama mafi tsadan dan'wasa na kowani lokaci.[8][9] A kakar sa na farko, Özil ya taimake kulub din Arsenal fc wajen samun kawo karshen tsawon shekara Tara ba tare da lashe gasa ba, inda suka lashe gasar kofin FA , lashe kofin a shekara ta 2014. Ya kuma kara samun yin nasarar lashe gasar Kofin FA biyu, da lashe FA garkuwan al u'uman . Özil ya kafa tarihi na Wanda yafi kowa yawan bada gudunmawa wajen cin kwallaye (assists) (19) a gasar kakan 'Premier League' a shekara ta 2014–15,da kuma sanya shi a cikin kungiyoyin kwararru da ake zaɓa daban-daban a kasar ingila.

File:20180602 FIFA Friendly Match Austria vs Germany Mesut Özil 850 0704.jpg
Ozil sanye da rigar garinsa Germany

A duniya kuma,Özil ya buga wasanni guda 92 ma kasar Jamus, ya kuma zura kwallaye 23,yayi taimako wajen cin kwallaye 40 assists.Ya kuma kafa tarihi na zama dan'kwallon kafa na ƙasar Jamus na shekara sau 5 (five German Player of the Year awards).Özil ya wakilci kasar sa a gasar FIFA World Cup guda uku(3),da kuma UEFA European Championship guda biyu (2),kuma yana daga cikin wadanda suka taka rawa a gasar shekara ta 2010 FIFA World Cup da gasar UEFA Euro a shekara ta 2012 a kasar South Africa da Ukraine,inda ya zama daya daga cikin mafi yawan taimako a dukkanin wasannin biyu (assist provider in both competitions). Özil ya kuma taimaka sosai a sanda kasar Jamus ta lashe gasar shekara ta 2014 FIFA World Cup a Brazil,inda ya samu plaudits for his versatility and creativity.Bayan gasar a shekara ta 2018 FIFA World Cup,Özil yayi ritaya daga buga wasa wa kasar sa, bayan yayi zargin nuna masa wariya da rashin girmamawa da German Football Association (DFB) tayi da kuma kamfanonin watsa labarai da suke kasar Jamus.

Manazarta gyara sashe

  1. "Ranking the best players in the Premier League". The Daily Telegraph. 2 November 2016.
  2. "Özil still 'one of the world's best' says Wenger". The Daily Telegraph. 13 October 2017.
  3. "Özil still 'one of the world's best' says Reus". Goal. 25 June 2018.
  4. "The top 10 assists leaders in Europe for 2010⁄11". imscouting.com. 30 May 2011. Archived from the original on 29 May 2012. Retrieved 30 January 2019.
  5. "Spanish La Liga". EXPN Soccernat.
  6. "Mourinho: Ozil will make history at Real". ESPNSTAR.com. 26 May 2012. Archived from the original on 28 June 2012. Retrieved 30 January 2019.
  7. "German international Özil joins Arsenal". Arsenal F.C. 2 September 2013. Retrieved 2 September 2013.
  8. Ornstein, David (2 September 2013). "Mesut Özil: Arsenal sign Real Madrid midfielder for £42.4m". BBC.
  9. "Arsenal smash club record to sign Mesut Özil". The Guardian. 2 September 2013. Archived from the original on 27 September 2013. Retrieved 30 January 2019.