Masarautar Katsina
Masarautar Katsina ta kasance babbar masarauta ce kuma mai daɗaɗɗen tarihi. Tana ɗaya daga cikin asalin garuruwan ƙasar Hausa. Kafin zamowarta wannan babban birni da a yau ya zama hedikwatar Jahar Katsina sannan kuma fadar masarautar jihar Katsina, ta taɓa zama a wani gari da yake da tazarar kimanin kilomita talalatin da biyu 32 daga Katsinan yau. Sunan wannan gari shi ne ‘Durɓi ta Kusheyi’. Wannan gari shi ne asalin fadar mulkin ddaular garin Katsina
Wannan masarauta cike take da ababen tarihi, a cikin wancan garin na Durɓi, akwai wannan kuka tana nan, akwai wani Dutse da su mutanen Durɓi suka taɓa bautawa, sannan akwai wata Hasumiya da ta haura shekaru ɗari shida (600) mai suna Gobarau a garin na Katsina. Kuma dai wannan gari shi ne matsugunnin tsohuwar makarantar da ta yaye firimiyan kasar Najeriya da kuma na Arewa ta farko. Wannan rubutu da ake karantawa zai bamu ƙarin haske game da wannan gari na garin Katsina.
Asalin Kafuwar Garin Katsina
gyara sasheBabu wata tsayayyar magana dangane da shekara, ko kuma haƙiƙanin mutumin da ya kafa wannan tsohon birni, mai tsohon tarihi na Katsina. Amma akwai hujjoji birjik (Ingawa,shekarar 2006; Lugga,shekarar 2004; Mamman, shekarar 2015), da ke tabbatar da tasowar fadar masarautar ta Katsina daga wani tsohon ƙauye mai suna Durɓi ta Kusheyi.
Katsina kamar sauran manyan masarautun ƙasar Hausa, gidan sarautarta yana da dangantaka da gidan Bayajidda.