Masallacin Abuja

Masallacin Ƙasa Abuja, wadda kuma aka fi sani da Masallacin ƙasa, Masallacin ƙasa ne a Najeriya.

An gina masallacin ne a shekarar 1984 kuma ya na buɗe wa jama'a waɗanda ba musulmi ba, amma ban da lokacin sallar jam'i.

An bai wa kamfanin 'Aims Construction Limited' kwangilar aikin gina masallacin kuma sun kammala aikin a shekarar 1984.

Tarihin masallacin ƙasa ya faro ne tun a shekarun 1980, lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya a lokacin mulkin mai girma shugaban ƙasa Shehu Usman Aliyu Shagari ta yanke shawarar tashi daga Legas zuwa sabon babban birnin tarayya Abuja.

A shekara ta 1981, wasu fitattun musulmi daga ko’ina a faɗin ƙasar sun bada shawarar cewa, al’ummar musulmi su nema da kuma karɓar gudunmowa daga gida da waje domin gina ginin masallaci a matsayin wurin ibada.

Manazarta

gyara sashe

abujanationalmosque.org