Malcolm Bidali wani mai fafutukar kare hakkin 'yan ƙwadago ne daga Kenya wanda ke mai da hankali kan yanayin da ma'aikatan baƙin haure ke fuskanta a Qatar. Bidali ya rubuta wa ƙungiyar Migrant-Rights.org, inda ya bayyana damuwa game da aiki da yanayin rayuwa da ma'aikatan baƙin haure ke fuskanta a Qatar da sauran ƙasashe. Hukumomin Qatar sun kama shi a shekarar 2021 saboda rubuce-rubucen da ya rubuta, kuma bayan an sake shi, ya yi tsokaci kan rashin kyawun tsarin gidan yari. Shi ne wanda ya karɓi lambar yabo ta shekarar 2023 Nuremberg International Human Rights Award saboda fafutukar kare haƙƙin ɗan adam. [1] [2] [3]

Malcolm Bidali
Rayuwa
Sana'a

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kenyan blogger: 'I thought I may never make it out of Qatar'". BBC News. September 16, 2021.
  2. "Migrant rights activist Malcom Bidali reveals details of Qatar arrest". DOHA News. September 19, 2021.
  3. "Kenyan guard who wrote on Qatar abuses fined, leaves country". AP News. August 19, 2021.