Makarantan Sekandare na kwana na Solomiya Krushelnytska Lviv

Makarantan Sekandare na musamman na kwana na Solomiya Krushelnytska Lviv makaranta ce na ilimi a Ukraine, inda dalibai suke koya ilimin Waƙa na musamman a matakin sakandare. An sanya wa makarantar suna ne bayan a soprano Solomiya Kruchelnytska.

Makarantan Sekandare na kwana na Solomiya Krushelnytska Lviv
Bayanai
Suna a hukumance
Львівська середня спеціалізована музична школа-інтернат імені Соломії Крушельницької.
Iri Makarantar allo da children's music school (en) Fassara
Ƙasa Ukraniya da Kungiyar Sobiyet
Adadin ɗalibai 411
Tarihi
Ƙirƙira 1939
solomiya-sk.lviv.ua

Makarantan Sakandare na Solomiya Kruchelnytska Lviv na kwana ƙwararriyar makaranta ce ta Waƙa a Lviv. An kafa makarantar a shekara ta 1939, a bisa shawaran mawaƙin Ukrainian kuma ɗan wasan pian Vasyl Barvinsky.[1] Kafin haka ana kiranta da Makarantar Empress Elisabeth kuma ta samo asalinta tun daga karni na sha takwas.[2] [3] Daga shekarar 1944, ta fara wanzuwa azaman makarantar sakandare don ɗaliban kiɗa; daga shekarar 1959, an sake tsara shi zuwa makarantar kwana ta kiɗa na musamman.[1] A shekarar 1963, makarantar da aka mai suna Solomiya Kruchelnytska.[1] Halyna Levytska ( uk ) ita ce darekta na farko na makarantar.[1] Daga shekarar 1972, zuwa 1997, darektan ya Volodymyr Antoniv.[1] A shekarar 1997 B. Martynovsky aka nada darektan, sai D. Komonko a shekarar 2004. Tun shekarar 2009 Lev Myronovych Zakopets ya zama darektan. [1]

Makarantar tana da sassan waƙa guda bakwai da ƙwararrun darussan waƙa sama da 20. An kafa darussa ta hanyar ilimi na gaba ɗaya, kiɗa-ka'idar da zagayawa na musamman.[4] Dalibai kuma suna nazarin wasu fannonin kiɗa, gami da: solfeggio, ka'idar kiɗa, jituwa, adabin kiɗa.[5] Makarantar tana koyarwa da harshen Ukrainian. Dalibai kuma suna koyon harsunan waje: Ingilishi, Faransanci, Jamusanci.[4] Makarantar tana da ƙarin albarkatu na ɗakunan kide-kide guda biyu, gidan kayan gargajiya na Solomiya Krusheelnytska, ɗakin karatu tare da tarin littattafai da tarin kiɗa. Leo Zakopets ya yi nazari kan salon koyarwa a makarantar da kuma muhimmancin waƙa wajen haɓaka yara.[6] Dalibai daga makarantar an san su da nasara a gasar kiɗa na ƙasa da ƙasa. [7]

Sanannun tsofaffin ɗalibai

gyara sashe

Fitattun tsofaffin ɗalibanta sun haɗa da:

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 "Львівська середня спеціалізована музична школа-інтернат ім. С. Крушельницької". www.akolada.org.ua. Retrieved 2021-03-01.
  2. "Solomiya Krushelnytska school of music". Urban media archive. Retrieved 2021-03-01.
  3. Гавеля, Оксана Миколаївна. "Діяльність творчої молоді України як реалізація культурних цінностей та духовних надбань сучасної цивілізації." Міжнародний вісник: Культурологія. Філологія. Музикознавство 2 (2014): 42-49.
  4. 4.0 4.1 "Lviv Secondary Special Music Boarding School named after S. Krushelnytska".
  5. "ЛССМШІ ім. С. Крушельницької - Львівська область. ІСУО". lv.isuo.org. Retrieved 2021-03-01.
  6. "Zakopets, Lev (2019-05-08). "MUSIC LESSONS AS A MAIN COMPONENT OF DEVELOPING CHILDREN'S MUSICAL TASTE IN LVIV SECONDARY SPECIALIZED MUSIC FORDING SCHOOL NAMED AFTER S. KRUSHELNITSKIY". Pedagogical Education: Theory and Practice. 2 (26): 76–79. doi:10.32626/2309-9763.2019-26-2.76-79. ISSN 2309-9763.
  7. Ємець, Наталія Анатоліївна. "Ідея Платона і Арістотеля як теоретичне підгрунтя неосхоластичної філософії доби українського бароко." Міжнародний вісник: Культурологія. Філологія. Музикознавство 2 (2014): 49-56.
  8. ImkaMusicCompetition (2019-03-30). "Daryna Bachynska". IMKA CLASSICAL MUSIC & DANCE COMPETITION AND CONCERT SERIES (in Turanci). Retrieved 2021-03-01.
  9. "Buriakovska Enhelina". UU Archive (in Turanci). Retrieved 2021-03-01.
  10. "OLENA HAVIUK-SHEREMET – #StayHome International Piano Competition" (in Turanci). Retrieved 2021-03-01.
  11. "Eva Rabchevska | VERE MUSIC FUND" (in Turanci). Retrieved 2021-03-01.
  12. "Vasyl Zatsikha | VERE MUSIC FUND" (in Turanci). Retrieved 2021-03-01.
  13. "Ustym Zhuk – alto". Lviv National Philharmonic (in Turanci). Archived from the original on 2022-02-28. Retrieved 2021-03-01. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)