MATAN DA SUKA HARAMTA A AURE:

:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

:

Assalamu Alaikum. Ina da yaya (wa) wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya da shi, sai ya auri wata bazawara, kuma ita ma tana da babbar ’ya. Shin ko zan iya auren wannan ’yar tata?

:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

:

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Da farko: Aure ba yana cikin babin Fiqhul-Ibaadaat ne, wanda ba a iya aikata komai a cikinsa sai da umurnin Allaah ko Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Amma yana cikin babin Fiqhul-Mu’aamalaat ne wanda ba a hana komai a cikinsa sai abin da Allaah ko Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hana. Don haka, kowace mace ya halatta musulmi ya aure ta in dai ba an samu wani dalili daga Allaah (Sabhaanahu Wa Ta’aala) a cikin Alqur’ani ko Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin Sahihan Sunnah ko wata ƙa’idar musulunci sun hana ba.

حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنَ الرَّضَاعَة  

An haramta muku auren uwayenku, da ’ya’yanku, da ’yan uwanku, da goggoninku, da innoninku da ’ya’ya mata na ’yan uwanku maza, da ’ya’ya mata na ’yan uwanku mata, da uwayenku waɗanda suka shayar da ku nono, da kuma ’yan uwanku mata na shan nono. (Surah An-Nisaa’: 23).

Manyan malaman musulunci da suka gama yin nazari a cikin Alqur’ani da Sunnah sun fitar da nau’ukan matan da ba su halatta musulmi ya aura ba. Da farko sun kasa matan gida biyu ne:

WAƊANDA SUKA HARAMTA HAR ABADA:

Akwai guda bakwai da suka haramta saboda dangantaka:

1. Duk macen da ta zama mahaifiya gare ka, kamar uwa da mahaifiyarta da kakanninta mata da mahaifiyar uba da kakanninsa mata.

2. Duk macen da kake matsayin mahaifi gare ta, kamar ’ya ko ’yar ’ya, ko ’yar da duk yadda suka yi ƙasa. Kuma wannan ’yar ko ta aure ne aka same ta ko ba ta aure ba ne.

3. Duk macen da ta haɗu da kai a asalin iyayenka, kamar ’yar uwa wacce ka haɗu da ita ta hanyar uwa da uba gaba ɗaya ko uwa kaɗai ko kuma uba kaɗai.

4. Duk macen da ta haɗu da mahaifinka ko kakanninka maza a asalin iyayensu: Ta fuskar uwa da uba gaba ɗaya, ko ta uwa kaɗai ko kuma uba kaɗai, kamar: Inna.

5. Duk macen da ta haɗu da mahaifiyarka ko kakanninka mata a asalin iyayensu: Ta fuskar uwa da uba gaba ɗaya, ko kuma ta uwa kaɗai ko uba kaɗai, kamar: Goggo.

6. Duk macen da ɗan’uwanka ya haife ta, ɗan’uwan nan ko shaƙiƙi ne ko wanda kuka haɗa uwa ce kaɗai, ko kuma wanda kuka haɗa uba ne kaɗai.

7. Duk macen da ’yar uwarka ta haife ta, ko ’yar uwarka shaƙiƙiya ce, ko wacce kuka haɗa uwa kaɗai, ko kuma wacce kuka haɗa uba kaɗai.

Akwai kuma guda uku da suka haramta ta fuskar surukuta:

1. Mahaifiyar matarka ko kakarta, da zaran an ɗaura maka aure da matar taka.

2. Matar ɗanka ko matar jikanka, da zaran an ɗaura musu aure.

3. Matar mahaifinka, da zaran an ɗaura musu aure.

Amma agolarka, watau ’yar da matarka ta haifa aurenta na zama haram gare ka ne kawai idan ka riga ka sadu da mahaifiyarta, watau matarka. Amma ba kawai domin an ɗaura muku aure, alhali ba ku tare da juna ba.

Sai kuma wasu nau’ukan mata guda bakwai da suka haramta ta dalilin shayarwa:

1. Matar da ta shayar da kai, da kakarta ta wajen uwa ko ta wajen uba.

2. ’Ya ko jikar matar da matarka ta shayar da ita.

3. Macen da mace ɗaya ta shayar da kai kuma ta shayar da ita.

4. ’Ya ko jikar matar da wata mace ta shayar da kai kuma ta shayar da ita.

5. ’Ya ko jikar namijin da wata mace ta shayar da kai kuma ta shayar da shi.

6. ’Yar’uwar mijin matar da ta shayar da kai.

7. ’Yar’uwar matar da ta shayar da kai.

Haka kuma duk matar da miji ya yi mata li’ani¹ a gaban alƙali, ita ma ta haramta gare shi har abada.

Li’ani wani nau’in sakin aure ne, inda miji da mata ke rantsuwa a gaban sarkin musulmi ko na’ibinsa, tare da yi wa junansu addu’ar aukuwar la’ana da fushin Ubangiji a kan maƙaryaci, saboda zargin rashin amincewa a tsakaninsu.

MATAN DA SUKA HARAMTA NA-WANI LOKACI:

Ga su kamar haka:

1. Haɗa ’yan uwa mata biyu ko fiye a wurin mijin aure ɗaya a lokaci guda. Amma idan auren ya mutu ko matar ta rasu, to zai iya auren ’yar uwarta.

2. Haɗa auren mace da innarta ko goggonta a wurin mijin aure ɗaya, sai dai ko in auren ya mutu ko matar ta rasu.

3. Matar auren wani, har sai ya sake ta kuma ta gama idda, ko ta gama takaba a bayan rasuwarsa.

4. Matarsa da ya sake ta saki na-uku, har sai bayan ta auri wani miji na-daban kuma ya sako ta a bayan ya sadu da ita saduwa ta haƙiƙa, kuma ta gama iddarsa.

5. Mushirika watau kafirar da ba Ahlul-Kitaab (Yahudu ko Kirista) ba, har sai lokacin da ta musulunta.

Akwai sharuɗɗa da malamai suka sanya kafin musulmi ya iya auren macen Ahlul-kitaab, wanda yawanci a yau mutane ba su cikawa, don haka suke ta samun matsaloli a bayan auren. Haka kuma haram ne mace musulma ta auri duk wanda ba musulmi ba ko da kuwa daga cikin Ahlul-Kitaab ne.

6. Auren wata mace ta-biyar a lokacin da yake tare da matan aure guda huɗu, har sai lokacin da ya rabu da wata ɗaya daga cikinsu kuma ta gama iddarta.

7. Ɗaura aure a lokacin da yake cikin harama da aikin hajji ko umurah, har sai lokacin da ya fita daga haramar.

8. Mazinaciya, har sai lokacin da ta tuba. Haka ma mazinaci ba za ta aure shi ba har sai ya tuba. Mazinata ma sai sun tuba.

A ƙarƙashin wannan bayanin kana iya auren ’yar da matar yayanka ta haifa, tun da ba ta daga cikin waɗannan matan da Allaah Ta’aala ya haramta aurensu. Sannan kuma dayake ba mu ga wata ƙa’ida daga cikin ƙa’idojin musulunci da ta hana hakan ba.

WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ