Louisa Motha
Louisa Motha ta kasance mai kula da ƙungiyar Abahlali baseMjondolo na shekaru da yawa tun daga shekara ta dubu biyu da hudu 2004. [1] Tana zaune ne a cikin ƙauyen Motala Heights a Pinetown kusa da birnin Durban dake yankin Afirka ta Kudu.[2][3]
Motha ta zama abokiyar ɗan gwagwarmaya Shamita Naidoo lokacin da suka haɗu suna wanke tufafinsu a cikin kogi.[4]
An san ta sosai da shirya adawa da korar mutane, kuma ta kasance mai sukar Dokar Slums. [5][6] Sa'annan kuma ta fara ƙungiyar kula da lambu ta mata da ake kira Motola Diggers . [4]
- ↑ Gunby, Kate (2007). "You'll Never Silence the Voice of the Voiceless: Critical Voices of Activists in Post-Apartheid South Africa". Independent Study Project (ISP) Collection. 115. Retrieved 22 September 2019.
- ↑ Gangster Landlord Continues Campaign of Intimidation with Local Police Support, LibCom, 2008
- ↑ All Charges Dropped Against the Pemary Ridge Thirteen, Interactivist, 2009[permanent dead link]
- ↑ 4.0 4.1 Pithouse, Richard (26 March 2014). "An Urban commons? Notes from South Africa". Community Development Journal. 49 (suppl 1): i31–i43. doi:10.1093/cdj/bsu013. Retrieved 22 September 2019.
- ↑ Symbol of Hope Silenced, Daily News, 2009
- ↑ UN Habitat Report on the Slums Act, 2008