Lois Auta (an haife ta ranar 29 ga watan Afrilu a shekarar 1980) ita ce ta assasa kuma ta kasance shugaban Gidauniyar Cedar Seed, kungiyar da ke bunkasa tarayyan mata masu nakasa a tafiyan ci gaban kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya. Tana mai da hankali kan dokokin da suka hada da mutane masu nakasa.[1]

Lois Auta
Lois Auta
Haihuwa (1980-04-29) 29 Afrilu 1980 (shekaru 44)
Jos, Nigeria
Wasu sunaye Nbwuat'ayan
Aiki activist
Shahara akan Rights of persons living with disabilities
Title Chief executive officer
Uwar gida(s) Mr Innocent
Yanar gizo cedarseedfoundation.org[dead link]

A cikin shekarar 2019, Auta ta yi takara a matsayin AMAC (Majalisar Yankin Abuja)/ Majalisar Dokoki ta Kasa na Bwari, a 2022 [2] ta nemi kujerar Kaduna State House of Assembly don wakiltar mazabar Kaura a ƙarƙashin dandalin jam'iyar All Progressives Congress wato (APC) amma ba ta samu nasaran lashe zaben ba inda ta fiskanci faduwA a zaben fidda gwani ga Nehemiah Sunday. Ta fuskanci nuna bambanci a matsayin miskiniyyar mace 'yar siyasa.[3][4]

Rayuwa ta farko

gyara sashe

An haifi Auta a garin Jos Plateau, Jihar Plateau dake Arewacin Najeriya a ranar 29 ga Afrilu 1980 a cikin zuriyan Auta Akok na Kukum Gida Kagoro.

Yayinda take yarinya, Auta ta kamu da cutar shan inna kuma an tsare ta a kan keken guragu. Tana da takardar difloma da digiri na farko a bangaren Gudanarwar Gwamnati daga Jami'ar Abuja, Najeriya . Ta yi karatun gudanar da harkokin kasuwanci na duniya a Jami'ar Nexford, da ke Washington, DC.

A cikin shekarar 2014, Auta ta shiga cikin Matasan Shugabannin Afirka kuma an zabe ta a matsayin abokiyar koyo na Mandela Washington [5]

  • Auta ta kasance wacce ta assasa kuma babban darakta na Cedar Seed Foundation.
  • Shugaban kungiyar wasanni masu nakasa dake FCT, Abuja
  • Memba na kwamitin Tarayyar Ma'aikatan Jama'a Ma'aikatan da ke da nakasa da yawa
  • Mataimakin Mai Gudanar da Ƙasa na Advocacy for Women with Disabilities Initiative
  • Memba na kwamitin Potters Gallery Initiative
  • Memba na Ƙungiyar Ƙasashen Mutane masu nakasa
  • Ta assasa Ability Africa
  • Shugaba na Women on Wheels Multipurpose Cooperative Society
  • Mataimakin shugaban kungiyar Mandela Washington Fellowship Alumni Association,Najeriya

A 2019, Auta ta nemi kujerar AMAC (Majalisar Yankin Abuja) / Bwari kujerar Majalisar Dokokin Kasa ta Babban Tarayya, kuma a cikin 2022, ta nemi samun kujerar majalisar dokokin Jihar Kaduna don wakiltar mazabar Kaura a ƙarƙashin dandalin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), amma ba ta rasa samu nasaran lashe zaben fidda gwani zuwa Nehemiah Sunday.[6] Ta fuskanci bambantaka kasancewa ta 'yar siyasa mace mai nakasa.

Manazarta

gyara sashe
  1. "President Buhari to host tech's brightest minds at Aso Rock". Nigerian Newspaper Toda. Retrieved 29 September 2016.
  2. Rapheal (2022-07-04). "Road to 2023: Why APC'll win 2023 poll –Lois Auta, founder of Cedar Seed Foundation". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-02-16.
  3. Ukwu, Jerrywright (2019-02-10). "Meet Lois Auta, a physically-challenged woman running for office in Abuja". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Archived from the original on 2020-08-11. Retrieved 2021-03-13.
  4. "From where I stand: "Disability will not stop me from achieving my dreams."". UN Women (in Turanci). 6 February 2019. Retrieved 2021-03-13.
  5. "Biographies-of-the-2014-mandela-washington-fellows". YALI. Retrieved 13 September 2022.[permanent dead link]
  6. Rapheal (2022-07-04). "Road to 2023: Why APC'll win 2023 poll –Lois Auta, founder of Cedar Seed Foundation". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-02-16.