Kayan Lefe Al’adar aure ce wadda ta samo asali a kasar Hausa wato dai Al'adar Hausawa ce inda ango ke siyan kayan amfani masu kyau da tsada a matsayin wata babbar kyauta da zai bawa amaryarsa. Wadannan kyaututtukan ango na gama sayen sune kafin Auren shi, bayan sun gama kammaluwa, sai iyayen Ango kama daga Inna, Gwaggonninsa da sauran su, mata ne suke kai kayan gidan Amarya, Ita kuma Amarya sai iyayen ta mata su karba kayan su dan ba iyayen Ango abinci da dan tukuici. Kayan Lefe a Auren Hausawa sunada matukar muhimmanci a yanzu, wanda ya kai a cikin Aure 100 da za'a daura a kasar Hausa, kuma na Hausawa to kaso 99.99% duk sai Ango yayi kayan lefe.[1][2] Al'adar wadda yanzu ta samu karbuwa sosai a cikin wasu yarurruka a yankin Arewacin Najeriya, don yanzu indai za'ayi Aure a Arewacin Najeriya ko na Hausawa ko ba Hausawa ba, to tabbas sai kaga kayan lefe a cikin auren.

Lefe
Kayan lefe a cikin akwatuna

Tarihin Lefe

gyara sashe

Asalin Lefe dai wata jaka ce da ake yinta da kaba, a zamanin da ya gabata ana zuba kayan kadi a cikin lefe, na sakar kaya wanda hausawa suke amfani dashi wajen saka kayan gargajiya. In muka duba bangaren aure kuma ana amfani da Wannan jakar don zuba kayan Aure wadanda ake kaiwa gidan iyayen amarya. Dalilin da yasa ake lefe shine don a girmama amarya, a mutunta ta, sannan tunda ance Amarya sabuwace to duk wasu kayan da za'a yiwa amarya sabbi ne, Kuma wannan nasa Aure yayi armashi. Ba anayi bane don a burge Amarya, ko don alfahari. Amfanin sa mai gida zai dauka lokaci bai sayawa matarsa kayan sawa ba. Zamanin da ya gabata ana amfani da jaka ta Kaba, sai aka koma amfani da jaka, sai fanteka, daro, kwalla, fantimoti, akwati mai taya, akwati mai fata, wanda yanzu akan wannan matsayin ake.[3]

Kayan Lefe

gyara sashe

A cikin lefe akwai kayayyakin amfani iri daban-daban ga wasu daga ciki:

  • Atampa
  • Leshi
  • Shadda
  • Hijabai
  • Gyale
  • Takalma
  • Dan kunne
  • Sarka
  • Yan ciki
  • Kayan bacci. Da dai sauransu.

Duk da muhimmanci da alfanun dake cikin al'adar, wasu suna ganin lefe a bangaren su baida wani alfanu duba da yadda tunanin lefe kan kange wasu matasan daga yin aure zuwa tsawon lokaci. Tabbas a wata mahangar lefe yana hana matasa yin Aure, a saboda haka ne ma yasa wasu yankunan suka soke lefe a a cikin sha'anin Aure, duk da cewa dai soke lefen baiyi tasiri wajen hana ayi shi kwata-kwata ba.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Daga baƙonmu na mako: Shin kayan lefe kyakkyawa ko mummunar al'ada ce?". BBC Hausa. 21 November 2020. Retrieved 21 December 2023.
  2. "Aure a Kasar Hausa". rumbun ilimi. Archived from the original on 24 January 2021. Retrieved 21 December 2023.
  3. "Daga baƙonmu na mako: Shin kayan lefe kyakkyawa ko mummunar al'ada ce?". BBC Hausa. 21 November 2020. Retrieved 21 December 2023.