Lansir ganye ne.

Amfani gyara sashe

Ganyen Lansir yana daya daga cikin ganyen da ake amfani da shi a duka faɗin duniya wajen sarrafawa ta fanni daban-daban, wasu sukan tafasa shi su sha Kamar ganyen shayin shan su a kullum, wasu kuma sukan yanka ganyen a saman abinci su ci.[1]

Har ila yau, wasu na amfani da ganyen lansir ba tare da sanin amfanin ganyen ga lafiyar jiki ba. Lansir dai ganye ne mai amfani sosai a jikin mutum, saboda yana tattare da sinadarai masu amfani ga lafiyar jikin mutum. Tabbas lansir ganye ne da yakamata mu cigaba da amfani da shi idan har kuma ba mu taba amfani da shi ba, yakamata mu fara amfani da shi saboda bincike ya tabbatar kuma ya nuna cewa yana da matukar amfani a jikin mu da kuma lafiyar mu.

Yanda ake sarrafashi gyara sashe

Za a samo ganyen lansir sai a tsaftace shi, a cire duk wani haki wanda ba a bukata daga gareshi, sai a yayyanka shi, a zuba masa ruwa kofi biyu, sai a tafasa shi, idan ya tafasa sai a sauke shi, a bar shi ya yi mintuna biyar, bayan ya huce sai a tace shi, a rika shan kofi ɗaya kullum da safe kafin a ci abinci.

Manazarta gyara sashe