Labarin Dujjal da Annabi Isa (A.S) 4

🌹🌹🌹

LABARIN DUJJAL DA SAUKOWAR ANNABI ISAH (AS) (4)

Yana cikin tsaka da haka ne sai Allah ya tayar da Annabi Isah dan Maryam عليه السلام. Annabi Isah عليه السلام zai sauko kusa da wata hasumiya fara gabas da Dimashqa (Syria) ya dora tafukansa biyu a kan fukafikan mala'iku guda biyu. Idan ya sunkuyar da kansa sai ruwa ya dinga diga, idan kuma ya daga kansa sai ruwa kamar lu'ulu'u ya gangaro. Duk kafirin da ya ji numfashinsa sai ya mutu, numfashinsa kuma yana kaiwa iyakar inda ganinsa ya kai. صلوات الله وسلامه عليك يا نبي الله!

Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Wata rana ina bacci sai na ganni a (mafarki) ina dawafi a Ka'aba sai ga wani mutum mai jan launin fata mai haske, mai laushin gashi, ruwa kuma yana diga daga kansa sai  na tambaya wane ne wannan? Sai aka ce da ni: Dan Maryam ne. Sai na juya na ga wani katon mutum mai jan launin fata mai kanadadden gashi, ba ya gani da idonsa na dama, idon kamar busasshen inibi. Sai na tambaya: "Wane ne wannan?" Sai aka ce da ni: "Wannan shi ne Dujjal". Annabi صلى الله عليه وسلم ya kara da cewa: "A cikin mutane wanda ya fi kama da Dujjal shi ne Ibn Qatan, wani mutum daga kabilar Khuzà'a."

Annabi Isah عليه السلام zai nemi Dujjal har sai ya gamu da shi a wata kofa da ake kira 'Babul-Lud' a kasar Falasdinu sai ya kashe shi.

Bayan nan sai Allah سبحانه وتعالى ya taimaki musulmi a kan Yahudawa sai su karkashe su har zata kai Bayahude zai buya a bayan dutse ko bishiya sai dutsen ko bishiyar su ce: "Ya kai musulmi, ga Bayahude a bayana zo ka kashe shi." Sai wata bishiya da ake kira Al-Garqada ita ce kadai ba zata fallasa su ba

Mutane zasu zauna bayan kashe Dujjal shekara bakwai babu adawa tsakanin mutum biyu.

Annabi Isah عليه السلام zai zama shugaba mai hukunci da adalci, zai jagoranci mutane da Alqur'ani da sunnar Annabi صلى الله عليه وسلم .....

                       الله تعالى اعلم

✍🏻 Umm Khaleel

                            🌹🌹🌹