Labarin Dujjal da Annabi Isa (A.S) 2

LABARIN DUJJAL DA SAUKOWAR ANNABI ISAH (AS) (2)

"Yana daga cikin fitinar Dujjal zai zo wajen wasu mutane ya kira su domin su yi imani da shi, sai su amsa masa su kuma yi imani da shi. Sai ya umarci sama sai ta yi ruwa, sai ya umarci kasa ita ma sai ta fitar da amfaninta, da yamma kuma sai dabbobin kiwonsu su dawo hantsarsu a cike sun yi kiba. Dujjal zai je wajen wasu mutanen sai ya kira su domin su yi imani da shi amma sai su ki, sai ya juya ya tafi sai su wayi gari cikin fari da yunwa babu komai a hannunsu na daga dukiyoyinsu.

Dujjal zai kuma wuce ta cikin hamada sai ya ce da ita ki fitar da taskokin arzikinki sai ta fitar, sai kuma kayan da fitar su bi shi kamar kudan zuma. Zai kuma kira wani matashi sai ya doke shi da takobi ya yanka shi gida biyu, bangarorin matashin guda biyu zasu rabu kwatankwacin tsawon mashi sai Dujjal ya kira shi sai kawai ya zo yana mai fara'a yana murmushi.

Dujjal zai zo Madina amma Ina! Allah سبحانه وتعالى ya haramta masa shiga, ba ma zai kusance ta ba, kuma duk wani tsoro da firgita na dujjal ba zai shiga Madina ba. A wannan lokacin Madina tana da kofofi guda bakwai a kowace kofa akwai mala'iku guda biyu.

Dujjal zai sauka a wani wuri kusa da Madina da ake kira "Sabakhah", sai wani mumini ya nufi wajensa sai ya hadu  da masu gadinsa dauke da makamai sai su ce masa: Ina ka nufa? Sai ya ce musu, zan je wajen wannan da ya bayyana ne. Sai su ce masa, "Shin ba kayi Imani da ubangijinmu ba ne?" Sai ya ce musu: "Ai alamomin Ubangijinmu ba sa buya." Sai wasu su ce, "Ku kashe shi." Sai wasu daga cikinsu su ce musu, "Shin ubangijinku bai hana ku kashe kowa ba?" Sai su tafi da shi wajen Dujjal. Idan wannan muminin ya gan shi sai ya ce: "Ya ku mutane! Wannan shi ne Dujjal wanda Annabi صلى الله عليه وسلم ya ambata." Dujjal sai ya bayar da umarnin a kwantar da shi a karya shi, sai kuma su rufe shi da duka ta gaba da ta baya. ....